Connect with us

Labarai

Ba ma goyan bayan abinda Rahma Sadau ta yi – Aminu S Bono

Published

on

Guda daga cikin ma su bayar da umarni a masana’antar Kannywood, Aminu S Bono, ya ce, abinda Rahma Sadau ta yi na wallafa hotunan da suka janyo cece-kuce a shafin ta na Istagram bai dace da tsarin addinin musulunci.

Aminu S Bono ya bayyana hakan ne cikin bacin rai a wani gajeren hoton faifan bidiyo na mintuna 8 da dakika 44 da ya fitar a shafin sa Instagram.

Ya ce, ”Rahma ki ji tsoron Allah abun da ki ka yi bai dace ba, ki gane cewa duniyar kadan ce rayuwar da za a yi a ranar lahira, ki zabi rayuwar da za ki dace, domin Annabi ya fada 60 ne zuwa 70”.

Ya kuma ce, “Rahma kafin a yi ki a cikin masana’antar nan an yi wa su da su ka fiki, yau sun rasu, yau babu Hauwa Ali Dodo, babu Hajiya Hauwa Maina, babu Rabilu Musa Dan Ibro”.

Ya kara da cewa, “A madadin mu na ‘yan fim ba ma goyon bayan ki ko kadan, kuma wallahi a kan a taba fiyayyen halita, Uwa da Uba da ‘ya’yan da a ka Haifa dukan su ba su da amfani a gareni, saboda Manzon Allah ya ce imanin dayan ku ba zai cika ba, sai ya so fiye da yadda ya so mahaifiya da mahaifi da ‘ya’yan sa, a gayawa Annabi magana ke ki je a dalilin ki wani ya yi magana mai muni a kan Annabi”.

Haka zalika, ya kuma ce, “Ina rokon miki shiriyar Allah, ni ba na kaunar duk wanda ya taba fiyayyen halite, kin a jawo mana matsaloli idan ba za ki shiryu ba, Allah ya hutar da ke sharrin ki, mun yi miki addu’ar shiriya, idan kuma ba haka ba Allah ya hutar da ke shiriyar ki”. A cewar Aminu S Bono.

 

Labarai

Shugabanni ku fito da sabbin dabaru domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta tsadar rayuwa a ƙasa – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights dake jihar Kano, ta ce akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya dace dan ganin an kawo karshen matsalar tsaro, da kuma ta harkar tsaro dake ci gaba da addabar mutane a sassa ƙasar nan.

Daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Laraba, ya ce yadda ake ƙara samun ƴan ta’adda suna sace mutane tare da kashe su a sassan ƙasar nan, da kuma halin matsin rayuwar da ake fuskanta akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya kamata dan ganin an kawo ƙarshen matsalolin.

“Yawaitar kai hare-haren da ake samu daga ɓangaren ƴan bindiga a cikin al’ummar gari akan kashe su tare da sace su matuƙar ana son a kawo karshen matsalar, sai an ƙara himma wajen samar da makamai ga jami’an tsaro tare da samar da sabbin dabaru domin kawar da matsalar, “in ji Galadanci”.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan da sako ɗalibai aƙalla su sama da 285, na makarantar Kuriga dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, da ƴan bindiga suka sace su a baya, baya ga wasu ɗaliban da aka sace a wata makarantar Tsangaya a jihar ta Kaduna, wanda ko a jihar Borno ma aka jiyo yadda aka sace ƴan gudun hijira da dama a baya-bayan nan, inda matsalolin tsaron ke ƙara yin gaba a sassan ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Kano ya kafa kwamitin duba yadda ake rabon tallafin abincin Azumi

Published

on

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin duba yadda ake ciyarwar azumin watan Ramadan, a kananan hokumomin cikin birnin jihar 8, domin sa ido da duba yadda ake gudanar da aikin dafawa da rabawa al’umma abincin.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin ne ƙarƙashin kulawar mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da wasu ƴan kwamitin.

Hakan na zuwa ne dai bayan da gwamna Abba Kabir, ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da ake dafa abincin, inda ya nuna rashin jin daɗin sa kan yadda ya ga aikin ke gudana a karamar hukumar kumbotso.

Bayanin hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwar da babban mai taimakawa gwamnan Kano, na musamman akan gidajen rediyo Bashir Aminu Fanshekara, ya aikowa manema labarai, ya ce an bayyana Alhaji Danyaro Yakasai, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin mai mambobi 7.

Fanshekara ya ce kwamitin ya fara zagayawa wasu daga cikin mazaɓu dake karamar hukumar kumbotso, domin duba yadda ake dafawa da kuma raba abincin tallafin ga al’umma, inda suka suka fara da mazaɓar Na’ibawa a ranar Asabar 23 ga watan Maris ɗin shekarar 2024.

Continue Reading

Ilimi

Kaduna:- Daliban Kuriga sun sha ki iskar ‘yanci

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da rahoton cewa an sako duka ɗaliban makarantar Kuriga da ƴanbindiga suka sace.

 

An sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna fiye da makonni biyu da suka wuce.

 

Sanarwar da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fitar ta ce an sako duka ɗaliban kuma suna cikin koshin lafiya.

 

Sanarwar ba tayi karin bayani ba game da irin matakan da aka bi wajen sako ɗaliban, sai dai gwamna Uba Sani ya nuna godiya ga shugaba Tinubu da mai bashi shawara kan tsaro da kuma sojojin Najeriya saboda irin rawar da suka taka wajen ganin an sako ɗaliban.

 

“Ba dare babu rana ina tattaunawa da Malam Nuhu Ribadu domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kubutar da daliban, kafin mu samu nasara,” in ji Uba Sani.

 

Galibinsu ɗaliban da aka sace ƴan shekaru biyar ne zuwa 18.

Continue Reading

Trending