Connect with us

Wasanni

Cristiano Ronaldo: PSG ta shirya daukan dan wasan – Leaonardo

Published

on

Daraktan wasannin kungiyar PSG, Leonardo ya tabbatar da cewa kungiyar a shirye ta ke tsaf domin daukan dan wasa Cristiano Ronaldo.

Ya ce”Har idan Ronaldo zai bar Juventus babu shakka mu ne za mu dauke shi a yanzu haka”. Inji Leonardo.

Ronaldo ya lashe gasar Firimiya da La Liga da kuma Serie A.

 

Wasanni

Club World Cup: Mun daga gasar zuwa sabuwar shekara – FIFA

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta tabbatar da daga gasar cin kofin kungiyoyin duniya na watan Dismabar shekarar 2020 zuwa watan Fabrairu na shekarar 2021.

Gasar za a gudanar da ita ne a kasar Qatar ranar 1 ga watan Fabrairu zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu sakamakon cutar Corona.

Zuwa yanzu zakarar gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai, Bayern Munich da kuma kungiyar Al-Duhail su ka tabbatar da shiga gasar.

Haka zalika hukumar FIFA ta tabbatar dakatar da gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan kasa da shekaru 20 da ‘yan kasa da shekaru 17 da za a gudanar a wannan shekarar.

Continue Reading

Wasanni

Tamaula: Mascherano ya jingine takalman sa

Published

on

Toshon dan wasan bayan Barcelona da Liverpool, Javier Mascherano ya rataye takalman sa daga harkokin Tamaula.

Dan wasan dan kasar Argentina mai shekaru 36 ya tabbatar da hakan ne a lokacin da ya shafe tsawon shekaru 17 a harkar kwallon kafa.

Mascherano, ya bugawa kasar sa wasanni 147 kafin ya dawo garin san a haihuwa inda ya bugawa Estudiantes de La Plata wasa a watan Janairu.

Continue Reading

Wasanni

Babu maganar zuwan Messi PSG – Mahaifin sa

Published

on

Mahaifin dan wasa Lionel Messi mai suna Jorge, ya yi watsi da rahoton da ke nuni cewa dan sa Messi ya tuntuni kungiyar Paris Saint-Germain domin ya koma taka leda.

Messi shekaru 33, na kokarin barin Barcelona a karshena kakar wasan nan wanda kungiyoyi da dama ke zawarcin sa.

PSG da Manchester City su ne dai su ka fara taya dan wasan tun bayan da Messi ya furta barin Barcelona.

Mai haifin Messi ya ce“A daina yada labaran kanzon kurege”. Inji Jorge.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!