Connect with us

Wasanni

Tsohon dan wasan Valencia da Madrid ya mutu

Published

on

Kafin mutuwar tsohon dan wasan Juan Cruz mai shekaru 73 ya taka leda a kungiyar Valencia inda ya buga mata wasanni har 400 daga shekarar 1965 zuwa 1981.

Cruz ya shafe tsawon shekaru 12 a Valencia ya kuma lashe kofin European Cup Winners da European Super Cup da Spanish Cup da kuma La Liga.

Ya kuma bugawa Madrid wasa na tsawon kaka biyar, inda ya lashe gasar La Liga 4, sannan ya bugawa kasar Andalus wasanni 28.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Club World Cup: Mun daga gasar zuwa sabuwar shekara – FIFA

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta tabbatar da daga gasar cin kofin kungiyoyin duniya na watan Dismabar shekarar 2020 zuwa watan Fabrairu na shekarar 2021.

Gasar za a gudanar da ita ne a kasar Qatar ranar 1 ga watan Fabrairu zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu sakamakon cutar Corona.

Zuwa yanzu zakarar gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai, Bayern Munich da kuma kungiyar Al-Duhail su ka tabbatar da shiga gasar.

Haka zalika hukumar FIFA ta tabbatar dakatar da gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan kasa da shekaru 20 da ‘yan kasa da shekaru 17 da za a gudanar a wannan shekarar.

Continue Reading

Wasanni

Tamaula: Mascherano ya jingine takalman sa

Published

on

Toshon dan wasan bayan Barcelona da Liverpool, Javier Mascherano ya rataye takalman sa daga harkokin Tamaula.

Dan wasan dan kasar Argentina mai shekaru 36 ya tabbatar da hakan ne a lokacin da ya shafe tsawon shekaru 17 a harkar kwallon kafa.

Mascherano, ya bugawa kasar sa wasanni 147 kafin ya dawo garin san a haihuwa inda ya bugawa Estudiantes de La Plata wasa a watan Janairu.

Continue Reading

Wasanni

Babu maganar zuwan Messi PSG – Mahaifin sa

Published

on

Mahaifin dan wasa Lionel Messi mai suna Jorge, ya yi watsi da rahoton da ke nuni cewa dan sa Messi ya tuntuni kungiyar Paris Saint-Germain domin ya koma taka leda.

Messi shekaru 33, na kokarin barin Barcelona a karshena kakar wasan nan wanda kungiyoyi da dama ke zawarcin sa.

PSG da Manchester City su ne dai su ka fara taya dan wasan tun bayan da Messi ya furta barin Barcelona.

Mai haifin Messi ya ce“A daina yada labaran kanzon kurege”. Inji Jorge.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!