Connect with us

Wasanni

Liverpool: Joe Gomez zai shafe tsawon lokaci ya na jinya

Published

on

An samu nasarar yi wad an wasan bayan Liverpool, Joe Gomez aiki a kafar sa tun bayan da ya samu rauni a kafar sa.

Kungiyar Liverpool ta tabbatar da cewa dan wasan zai shafe tsawon lokaci bai bugawa kungiyar wasa ba a gasar Firimiya.

Dan wasan Gomez ya samu rauni ne yayin da yak e daukar horo da kasar sa ta Ingila.

Gomez mai shekaru 23 ya ji raunin ne a gwiwar kafar sa ta hagu wanda tuni an samu nasarar yi masa aiki.

Yanzu haka dan wasan ya bi sawun Virgil van Dijk wanda shi ma ya ke fama da rauni a kafar sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Club World Cup: Mun daga gasar zuwa sabuwar shekara – FIFA

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta tabbatar da daga gasar cin kofin kungiyoyin duniya na watan Dismabar shekarar 2020 zuwa watan Fabrairu na shekarar 2021.

Gasar za a gudanar da ita ne a kasar Qatar ranar 1 ga watan Fabrairu zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu sakamakon cutar Corona.

Zuwa yanzu zakarar gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai, Bayern Munich da kuma kungiyar Al-Duhail su ka tabbatar da shiga gasar.

Haka zalika hukumar FIFA ta tabbatar dakatar da gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan kasa da shekaru 20 da ‘yan kasa da shekaru 17 da za a gudanar a wannan shekarar.

Continue Reading

Wasanni

Tamaula: Mascherano ya jingine takalman sa

Published

on

Toshon dan wasan bayan Barcelona da Liverpool, Javier Mascherano ya rataye takalman sa daga harkokin Tamaula.

Dan wasan dan kasar Argentina mai shekaru 36 ya tabbatar da hakan ne a lokacin da ya shafe tsawon shekaru 17 a harkar kwallon kafa.

Mascherano, ya bugawa kasar sa wasanni 147 kafin ya dawo garin san a haihuwa inda ya bugawa Estudiantes de La Plata wasa a watan Janairu.

Continue Reading

Wasanni

Babu maganar zuwan Messi PSG – Mahaifin sa

Published

on

Mahaifin dan wasa Lionel Messi mai suna Jorge, ya yi watsi da rahoton da ke nuni cewa dan sa Messi ya tuntuni kungiyar Paris Saint-Germain domin ya koma taka leda.

Messi shekaru 33, na kokarin barin Barcelona a karshena kakar wasan nan wanda kungiyoyi da dama ke zawarcin sa.

PSG da Manchester City su ne dai su ka fara taya dan wasan tun bayan da Messi ya furta barin Barcelona.

Mai haifin Messi ya ce“A daina yada labaran kanzon kurege”. Inji Jorge.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!