Connect with us

Labarai

Tsaro: Gamayyar kungiyoyin Arewa sun ce shugaba Buhari ya gaza

Published

on

Gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) ta bayan matsayin kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) kan kalubalen tsaro da ke ci gaba a arewacin Najeriya, tana mai cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kasa magance babban aikin da ke gabansa na samar da tsaro.

Kakakin gamayyar kungiyoyin, Abdul-Azeez Suleiman, yayin da yake maida martani a ranar Talata, ya ce dole ne al’ummomin arewacin Najeriya su nemarwa kansu mafita, don kare kansu.

“Al’umomin Arewa suna fama da barazanar‘ yan fashi da masu satar mutane, manyan titunan mu babu ingancin tsaro, mazauna kauyuka suna gujewa yankunansu kuma abinda muke gani shine, shugaban kasa ya gaza kuma da gangan baya yarda da shawarar mafi yawan ‘yan Najeriya na korar shugabannin hafsoshin tsaro, ”in ji shi.

Ya ce ya zama dole yanzu ga al’ummar Najeriya su hada kai kan yadda za su kare kansu saboda‘ yan fashin, sun fatattaki mutane daga gidajen su kuma hatta wurare kamar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da Nuhu Bamali Polytechnic ba su da tsaro kuma wannan na zuwa ne a wani lokaci cewa wataƙila ɗalibai za su koma makaranta. Abin da wannan ke nufi shi ne iyaye da ke kokarin hanzarta tura yaransu makaranta, dole ne su tabbata cewa an tsare rayuwarsu.

Arewa ta fusata da Buhari kan rashin tsaro

A ranar Litinin ne kungiyar ta ACF ta bayyana bacin ran ‘yan arewa ga Shugaba Buhari kan yadda kalubalen tsaro ya kara kamari a yankin.

Sakataren yada labarai na ACF na kasa, Emmanuel Yawe, ya ce ‘yan arewa sun yi tsammani da yawa daga wannan gwamnati mai ci.

“Gwamnati ba ta da himma kuma ya kamata ta dogara da rahotannin sirri. A mafi yawan lokuta, muna samun labarin abinda ke faruwa a hanyar Kaduna zuwa Abuja sannan za mu ji cewa akwai wani mummunan hari a can, amma kamar ba sa tattara isassun bayanan sirri, shi ya sa ‘yan fashi da’ yan Boko Haram suke gaba da gaba sosai su.

Yawe ya ce: “Mun san cewa gwamnatin da ta gabata ta rikita batun tsaro kuma mun san hakan saboda shugaban kasar na wancan lokacin ba shi da masaniyar tsaro, kawai malamin jami’a ne da ya tsunduma cikin siyasa kuma ta wata hanya ya zama shugaban kasar. Amma wannan, Shugaba Buhari shi ne wanda ya yi yakin basasa kuma wanda lokacin da ’yan Chadi suka mamaye Nijeriya suka fatattake su a lokacin mulkin Shagari, don haka a bayyane yake, yana da kwarewa sosai na kula da tsaron kasar nan,” in ji shi.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending