Connect with us

Labarai

PDP – Bashir Sanata ya zama jami’in hulda da jama’a

Published

on

Jam’iyar PDP a jihar Kano ta nada Bashir Aminu V.I.O wato Bashir Sanata a matsayin sabon jami’in hulda da jama’a na jam’iyar.

Zaben wanda ya gudana a yau Litinin a Lugard dake unguwar Nasarawa GRA wanda a ka zabi, Alhaji Shehu Sagagi a matsayin shugaban jami’yar, yayin da Dankaka Hussaini Bbebeji ya zama mataimakin jam’iyar.

Ga jerin zababbin sunayen ‘ya’yan jam’iyar kamar haka:

1- Alh. Shehu Sagagi

Chairman

  1. Hon. Dankaka Hussaini Bebeji

Deputy Chairman

  1. Hon. Hamisu Saad Dogonnama

Vice Chairman Kano Central

  1. Hon. Hashim Sulaiman Dungurawa

Vice Chairman Kano North

  1. Hon. Mukhtar Dankadai

Vice Chairman KanoSouth

  1. Hon. Jamilu Abubakar Danbatta

Secretary

  1. Hon.Yusuf Ibrahim Abubakar

Assistant Secretary Kano Central

  1. Hon. Jamilu Garba Garo

Asistant Secretary Kano-North

  1. Hon. Abba Abubakar Wudil

Assistant Secretary Kano-South

  1. Hon Idris Zare Rogo

Treasurer

  1. Hon. Sani Gora

Assistant Treasurer Kano-Central

  1. Hon. Magaji Uba Yalwa

Assistant Treasurer Kano-North

  1. Hon. Umar Maigoro Rano

Assistant Treasurer Kano-South

  1. Hon. Dahiru Maitama Arrow

Financial Secretary

  1. Hon. Auwal Garko

Assistant Financial Secretary

  1. Hon. Bashir Sanata

P.R.O

  1. Haj. Bintoto Kofar Ruwa

Assistant P.R.O

  1. Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso

Organizing Secretary

  1. Hon. Adamu Ali Ibrahim

Asst. Organizing Sec. Kano-South

  1. Hon. Ismail Sabo Abba

Asst. Organizing Sec. Kano-Central

  1. Hon. Abubakar Sulaiman Mairogo

Asst. Organizing Sec. Kano-North

  1. Barr. Wangida Isah

Legal Adviser

  1. Barr. Amina Umar Garba

Assistant Legal Adviser

  1. Hajiya Halima Uba Jalli

Women Leader

  1. Mariya Sani Karaye

Assistant Women Leader Kano-South

  1. Haj. A’isha Jafaru Fagge

Assistant Women Leader Kano-Central

  1. Haj. Aina’u Muhammad Bichi

Assistant Women Leader Kano-North

  1. Hon. Hafizu Sharif Gambo

Youth Leader

  1. Hon. Nura Ali Doguwa

Assistant Youth Leader Kano-South

  1. Hon. Kabiru Haruna Getso

Assistant Youth Leader Kano-South

  1. Hon. Shamsu Aliyu Samanja

Assistant Youth Leader Kano-Central

  1. Hon. Auwalu Nagero

Auditor

  1. Haj. Atine Abdullahi

Assistant Auditor

  1. Rabiu Sarkin Fulani

Ex-officio

  1. Faruk Gwadabe

Ex-officio

  1. Sabo Yau Yaura

Ex-officio

  1. Haj. Habiba Abdullahi Takai

Ex-officio

  1. Hajiya Mama Dorayi

Ex-officio

  1. Haj. Balaraba Sani Lawan Bagwai

Ibrahim Adam

Wakilin mu Abba Haruna ya tabbatar mana da cewa tuni sababbin jagororin jam’iyar su ka fara aiki nan take har zuwa tsawon shekaru hudu a nan gaba.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending