Connect with us

Labarai

Zargin lauya da cinye kudin fili: Kotu ta sanya wata gobe domin sauraron shari’a

Published

on

Babbar kotun jiha mai zamanta a karamar Hukumar Rano, karkashin mai Shari’a Abdu Mai Wada ta sanya ranar 28 ga watan gobe dominn fara sauraron wata sharia wadda wani mai suna Ibrahim Abdullahi ya shigar yana karar wani lauya mai suna barrister Ibrahim Baban gida.

Ibrahim Abdullahi dai ya shigar da kara ne yana rokon kotu da ta sanya a dawo masa da kudinsa miliyan 8 da dubu dari 7 wanda ya sayi wani fili mallakin Alhaji Bukar Gana a kan kudi Naira miliyan 20 sakamakon rashin biyan kudin a kan lokaci aka sayar wa da wani mutum filin.

A zaman kotun na ranar Laraba wanda aka yi kara ta bakin lauyansa sun roki a sanya Muhammad umar cikin kunshin wadanda ake kara kasancewar kudin da ake nema suna hannusa.

Sai dai wakilinmu Yusuf Nadabo ya tuntubi wanda ake kara barrister Ibrahim Babangida wanda ya bayyana cewar tabbas mai kara ya biya kudi ta hannunsa kuma ya bashi rasiti amma wadannan kudi an tura su asusun wani mutum wanda aka fara sayarwa da filin daga baya ciniki ya tashi an kuma tura kudin da yaddar shi mai kara Ibrahim.

Wakilin namu ya sake tambayar lauyan batun inda kudin Ibrahim Naira miliyan 8 da dubu Dari 7 suka makale sai lauyan ya shaida masa kudi suna hannun Muhammad umar tunda shi ne ya sayar da filin ba tare da masaniyar su ba. Dan haka ne ma suka roki kotu da ta amince a sanyo shi cikin wadanda ake kara.

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending