Connect with us

Labarai

Iyaye sai sun ƙara kula da ƴaƴan su domin gudun gurɓacewar tarbiyya – Sheikh Mukhtar

Published

on

Wani malamin addinin musulunci a jihar Kano Sheikh Muhktar Salisu, ya yi kira ga iyaye da su ƙara kulawa da samarin da suke zuwa wajen ƴaƴan su mata, domin gudun gurɓacewar tarbiyyarsu.

Sheikh Mustapha Salisu ya yi kiran ne a yayin saukar karatun Al’ƙur’ani mai girma da makarantar Ma’ahad Abdullahi Hassan ta gudanar cikin unguwar Waika Waje Yamma Maƙabartar Daɓai a yankin ƙaramar hukumar Gwale da ke Kano, wanda ya gudana a ranar Lahadi.

Yana mai cewa, “Matuƙar iyayen za su ƙara kulawa da samarin da ƴaƴan nasu mata suke tare da su, babu shakka za’a samu raguwar lalacewar ƴan mata da a kan samu a wannan zamani”. A cewar Sheikh Mukhtar Salisu.

Da yake nasa jawabin Mallam Bashir Gwani Azare, kira yayi ga al’ummar musulmai da su ƙara ƙaimi wajen haddace Al’ƙur’ani mai girma, domin rabauta da rahmar Allah S.W.T.

Mallam Mustapha Abdullahi Hassan, shi ne shugaban makarantar, ya ce “A mafi yawan lokuta mu na fuskantar ƙalubale daga wajen iyaye wajen turo ƴaƴansu a kan lokaci, saboda haka ya buƙaci da su rinƙa turo su makaranta a kan lokaci, domin samun ingantaccen ilmi”. Inji Malam Mustapha.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Ɗalibai kimanin 17 ne suka yi saukar Karatun Al’kur’anin mai girma masu ƙarancin shekaru da basa wuce shekaru 12, 11, da kuma 13 yayin da suka kasance maza 10 mata 7.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending