Connect with us

Labarai

Sada zumunci zai sanya al’umma rabauta da rahamar Ubangiji – Dr Surajo Sagagi

Published

on

Wani malamin Addinin musulunci a jihar Kano Dakta Surajo Sani Sagagi, ya buƙaci al’ummar musulmai da su ƙara kaimi wajen sada zumunci a tsakaninsu.

Dakta Surajo ya buƙaci hakan ne a yayin taron sada zumunci da iyalan Marigayi Mallam Haruna Musa, suka gudanar a ɗakin taro na Islamic Center da ke unguwar Ƙofar Kudu a yankin ƙaramar hukumar Garko, a karshen makon da ya gabata.

Yana mai cewa, “Matuƙar al’umma za su ƙara riko da sada zumunci, babu shakka zasu sadu da rahmar Allah S.W.T, a nan duniya dama ranar gobe ƙiyama”. A cewar Dakta Sirajo Sani Sagagi.

A nasa ɓangaren Mallam Sulaiman Haruna, wanda ya kasance ɗaya daga cikin dattawan yankin, kira ya yi ga iyaye da su rinƙa tura ƴaƴansu gidajen ƴan uwa, domin ƙara sanin juna a tsakani.

Da yake nasa jawabin Sakataren shirya taron Khamis Sani Haruna Musa, cewa ya yi sun shirya taron ne domin ƙarfafa zumuncin da ke tsakaninsu, kuma sun shirya tsaf wajen ganin an ci gaba da shirya irin wannan taro duk shekara, domin ƙara sanin juna.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Iyalan Marigayi Mallam Haruna Musa da dama ne suka halarci taron daga jahohi 7, wanda suka fito daga jahohin Adamawa, Nasarawa, Katsina, gami da kuma Abuja, da dai sauransu, wanda suka nuna farin cikinsu bisa yadda suka haɗu da junansu.

Labarai

Gwamnatin Kano za ta inganta filaye da bunƙasa duk ɓangarorin wasannin matasa – Kwamishinan Matasa da Wasanni

Published

on

Sabon kwamishinan ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa na Jihar Kano Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya bada tabbacin cewar Gwamnatin Jihar za ta ɗauki matakin inganta filayen tare da bunƙasa duk wasu ɓangarorin wasanni da matasa ke yi.

Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki yau Asabar, tare da kai ziyara a wasu filayen wasannin dake ihar Kano.

Daga cikin filayen wasannin da ya ziyarta akwai filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata, da filin wasa na Kano Pillars da ke sabon Gari, da kuma filin wasa na Ado Bayero Square dake unguwar Sabon Gari, sai kuma filin wasa na Mahaha da ke ƙofar Na’isa.

Da yake jawabi bayan kammala ziyarar kwamishinan wasannin da ci gaban Matasa na jihar Kano, Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya ce ya gudanar da ziyarar ce domin sanin halin da filayen wasannin ke ciki.

A lokacin ziyarar kwamishinan na tare da mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan harkokin wasanni Ambasada Yusuf Imam Ogan Ɓoye, da shugaban magoya bayan ƙungiyar ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars Alhaji Rabi’u Abdullahi Kawo, da kuma mai riƙon Shugabancin hukumar wasanni ta jiha Malam Bala Sani Shehu.

Continue Reading

Labarai

Muna sane da ƙarancin Ruwa a wasu sassan Kano – Hukumar rarraba ruwan Sha

Published

on

Hukumar rarraba ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin samun ruwa da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kano, yana da alaƙa ne da lalacewar wani abun kan Famfo a madatsar ruwan da ke Tamburawa.

Shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka yayin zantawar sa da manema labarai, ya ce cikin guraren da za’a yiwa gyaran har da madatsar ruwa ta Challawa da Watari, da amincewar gwamnatin jihar Kano.

Injiniya Garba, ya kuma ce suna sane da ƙarancin ruwan da ake fuskan ta a wasu sassan jihar Kano, amma nan gaba kaɗan za kammala gyaran kan famfon, domin ganin an wadata sassan jihar Kano, da ruwan domin ganin sun samu wani sauƙi.

 “Mu ma a ɓangaren mu Bama jin daɗin yadda al’umma suke rasa ruwa a sassan jihar Kano, kuma nan da ranar Litinin mutane za su fita daga cikin wannan matsala ta rashin Ruwa, a yanku nan su, “in ji shi”

Garba Ahmad, ya kuma ƙara da cewa matsalar fashewar Fayif da aka samu a ci gaba da aikin gadar mahaɗar Ɗan Agundi, yanzu haka suna kan ɗaukar mataki tsakanin su da kamfanin da suka taka har ya fashe, dan ganin an gyara al’ummar da ake baiwa ruwa su ci gaba da damu.

Continue Reading

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Trending