Wasanni
Kwallon kafa: Za a fara gasar Abubakar Zakari PA

A ranar Lahadi ne za a fara gasar cin kofin Hon Abubakar Zakari Muhammad PA a filin wasa na asibitin Aminu Kano dake yankin karamar hukumar Tarauni.
Cikin wata sanarwa da mai horaswa Umar Zeeba kuma wanda ya shirya gasar ya sanyawa hannu, sanarwar ta ce za a fara wasan farko ne tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Unguwar Gano da kuma Gyadi-Gyadi Kudu da karfe 9 na safiyar ranar.
Kungiyoyi goma ne na cikin mazabun karamar hukumar Tarauni za su fafata a cikin gasar.
Ma horaswa Umar Zeeba, ya kuma ce sun shirya gasar ne a yankin Tarauni domin bunkasa harkokin wasanni tun daga matakin tushe.
Wasan dai Hon Abubakar Zakari Muhammad PA shi ne ya dauki nauyin gasar, domin farfado da kwallon kafa tare da hada kan matasa a yankin karamar hukumar Tarauni.
Yayin take wasan farko a na sa ran halartar babban bako na musamman kwamishinan harkokin shari’a na jihar Kano, Barrista M.A Lawan da kuma dan majalisa mai wakiltar mazabun yankin karamar hukumar a tarayya, Hon Hafizu Kawu.
Wasanni
Wasan Golf: Yadda matasa su ka karbi wasan Golf a Kano

Wasu matasa a jihar Kano da suke wasan kwallon Golf sun ce a yanzu haka sun karbi wasan Golf a matsayin wasan da za su nuna bajinta a cikin kwallon Golf.
Daga filin wasan kwallon Golf na Kano Club wakilin mu Musa Abdu Tudun Wada ya turo mana da rahoto.
Wasanni
Division 2: Sakamakon gasar a Kano

Sakamakon gasar Division 2 da ake fafatawa a jihar Kano.
Affar Utd ta doke Fc Mai Kwai da ci 1-0
Jarma Fagge – 2 All Star Yan kaba- 1
Fc Milo – 0 Dan Dalama – 3
Mujan Warriors – 2 Fc Yelwa – 0
Mabusa Fc – 1 Blue Star Unguwa Uku – 2
Jakada Utd – 1 Ajingi Unted – 0
Golden Star Bunkure – 3 Junior Highlanders – 2.
Wasanni
Kano: Gasar Unity Cup da Divison Two

A gasar cin kofin Unity na kakar 2020 da 2021 da ake fafatawa a jihar Kano.
Kungyar kwallon kafa ta Zoo United ta yi rashin nasara da ci biyu da nema a hannun Super Star Sheka. Dan wasa Nasiru Shamalala shine ya jefa kwallon farko minti 21 yayin da Babu Messi ya jefa kwallo ta biyu 79.
A wasan sada zumunci da za a fafata a yammacin Juma’a.
Kungiyar kwallon kafa ta FC Rising Stars za ta barje gumi da New Stars FC
A filin wasa na New Star.
Mazugal United za ta karbi bakwancin FC Kofar Ruwa a filin wasa na Kofar Mazugal filin Holo.
ita kuwa FC Sharifai Academy kece raini za ta yi da Ahmad Academy a yammacin ranar Lahadi a filin wasa na Ramcy dake kwalejin Rumfa.
A gasar cin kofin ajin matasa na rukuni na daya wato Divison One cikin rukuni na 8 da za a fafata a yammacin gobe.
Old Star Dawakin Kudu da FC KAROTA a filin wasa na biyu dake Mahaha.
Gaida United za ta kara da Tango United a filin wasa na Kano United dake Mahaha.
ADS FC za ta kece raini da Zage United a filin wasa na Sharada United dake Mahaha.
A rukuni na 9 kuwa a cikin gasar, Dala United da Kurna FC a filin wasa na Sagagi dake Mahaha.
National Star Dukawa za ta gwada kwanji da Super Real a filin wasa na Diso United dake Mahaha.
A yayin da Fantel FC za ta kara da Junior Pillars ‘yan kasa da shekaru 15 a filin wasa na hudu dake Mahaha.
-
Manyan Labarai11 months ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi1 year ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai11 months ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi1 year ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai12 months ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari
-
Nishadi1 year ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Labarai3 months ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai12 months ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
You must be logged in to post a comment Login
You must log in to post a comment.