Connect with us

Labarai

Rediyon Dala ta na baiwa matasa gudunmawa – Kungiyar masoya Dala

Published

on

Shugaban Ƙungiyar masoya tashar Dala FM Kano Mansur Tallman mai Faci, ya bayyana gida gidan rediyon Dala a matsayin gidan da yake bada gudunmawa ga al’umma musamman ma matasa.

Mansur Tallman ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan tashi daga taron sada zumunci da suka shirya tare da ma’aikatan tashar da kuma masu sauraron tashar, wanda ya gudana a Lahadin makon da ya gabata a makarantar Ɗandago dake yankin karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Yana mai cewa, “Babu shakka gidan rediyon Dala FM Kano, ya yi fice wajen wa’azantarwa, faɗakarwa, harma da Nishaɗantar da al’umma, shiyasa muka ƙirƙiri Ƙungiya ga masu sauraron tashar domin ƙara ƙarfafa zumunci a tsakanin”.

Ya kuma ce, “Mun karrama ma’aikatan tashar ne bisa yadda suke ƙoƙari wajen ilmantar da al’umma a yayin gudanar da aikinsu”. A cewar Mansur Tallman.

Da yake nasa jawabin shugaban tashar Dala FM Kano Mallam Ahmad Garzali Yakubu, wanda ya samu wakilcin ɗaya daga cikin ma’aikatan tashar Munnirat Sule Garko, miƙa godiyarsa ya yi ga shugabannin Ƙungiyar harma da dukkanin masu sauraren tashar bisa samun damar halartas taron da sukayi, inda yace yana alfahari da dukkanin masu sauraron tashar ta Dala FM Kano.

A yayin taron dai Ƙungiyar ta karrama wasu daga cikin ma’aikatan tashar Dala FM Kano, waɗanda suka haɗar da Tijjani Adamu, Munnirat Sule Garko, Abdulƙadir Yusif Gwarzo, da kuma Muhammad B Umar Hankaka, da dai sauran wasu ma’aikatan, harma da wasu daga cikin masu sauraron tashar.

Wakilin mu da ya halarci taron Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Al’umma da dama ne suka halarci taron daga sassa daban daban na jihar Kano, harma da wasu jahohin ƙasar nan, da suka hadar da Jihar Legas, Katsina, Harma da Jigawa da dai sauransu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Ina zargin mai sayar da fili ya bani takardar Biredi – Wata Mata

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu, wata mata ta yi karar wani mutum da cinye mata Filaye guda takwas ta hanyar ba ta takardun bogi.

Sai dai kafin fara shar’ar ne kotun ta samu sanarwar dakatar da gudanar da shari’a saboda hutu da kotunan jihar Kano su ka tafi a ranar ta Talata.

Saurari wannan domin jin cikakken rahoton.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotunan jihar Kano na jiran umarnin tafiya hutu a rubuce – Baba Jibo

Published

on

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya tabbatar da umarnin rufe kotunan jihar Kano a ranar Talata.

Sai dai Baba Jibo Ibrahim a yayin zantawarsa da wakilin Ibrahim Abdullah Sorondinki ya ce, suna jiran umarnin ne a rubuce domin sanar da kotuna da kuma sauran al’umma akan halin da ake ciki.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: ‘Yar kasuwa ta gurfana a kotu kan zargin cinye manyan Kudade

Published

on

Babbar kotun shari’ar musulunci da ke filin Hockey karkashin mai shari’a Abdullahi Halliru Abubakar, ta gurfanar da wata mata kan zargin karbar kudi Naira miliyan tara da dubu dari shida a hannun wani mutum da zummar za su yi harkar kasuwancin Dala.

Mutumin mai suna Musa Yusuf Abubakar yana karar matar mai suna Farida Usman Dantata, da cinye kudaden, wanda kuma kasancewar ranar Talatar hutu a ke yi mai shari’a bai zo ba, aka dage shari’ar zuwa ranar biyu ga watan uku shekarar 2021.

Domin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!