Connect with us

Labarai

Iyaye su ƙara ƙaimi wajen karantar da ƴaƴansu Alƙur’ani – Sarkin Ban Kano

Published

on

Sarkin Ban Kano Hakimin Ɗan Batta Alhaji Isyaku Wada Waziri Ibrahim, ya gargaɗi iyaye da su ƙara kulawa da karatun ƴaƴansu, domin rayuwarsu ta zamo abar koyi.

Alhaji Isyaki Wada ya bayyana hakan ne a yayin saukar karatun Alƙur’ani mai girma, da makarantar Ibn Khasir Littahafiz Qur’an Waddirasatul Islamiyya na ɗalibai 48, da ta gudanar cikin unguwar Ja’en dake yankin ƙaramar hukumar Gwale a ƙarshen makon da ya gabata.

Yana mai cewa, Ƙara kulawa da karatun ‘ƴay’an nasu zai taima wajen kaucewarsu daga faɗawa cikin wani halin rayuwa, kuma al’ummar musulmai sai sun kara kaimi wajen riƙo da Alƙur’an mai girma, domin duk wanda yabar Alƙur’ani, to babu shakka shima kuwa zai bar shi.

A nasa jawabin shugaban makarantar Mallam Salmanu Rabi’u bayyana farin cikinsa ya yi, tare da yin kira ga iyaye harma da gwamnati da su shigo su tallafawa makarantar da mazauni, da kayayyakin da za su taimaka wajen tafikar da al’amuran makarantar, bisa ƙarancinsu da suke fama dasu.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Al’umma da dama ne suka halarci Bikin Saukar Alƙur’anin, daga ciki kuwa akwai Ɗan Majen Kano Hakimin Gwale Alhaji Yahya Inuwa Abbas.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending