Connect with us

Labarai

Ganduje ya jaddada yunkurin gwamnati na gyaran gidaje da filaye mallakarta

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ce, tana nan kan yunkurinta na gyara duk wasu gidaje ko filaye mallakin gwamnati wadanda ba a amfani da su domin samarwa da gwamnati kudin shiga.

Kwamishinan shari’a kuma Atoni janar na Kano Barista Lawan Abdullahi Musa ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin zantawarsa da manema labarai.

Yana mai cewa, “Ya yi mamaki yadda kungiyar ma’aikatan kotu suka gurfanar da gwamnati a gaban babbar kotun Kano kasancewar su na da masaniya kan yadda tsarin shigar da kara wadda ta shafi al’amuran albashin ma’aikata amma suka yi haka”.

Ya kuma ce, “Kotun da’ar ma’aikata ce kadai keda hurumin sauraron karar da kungiyar ma’aikatan kotuna suka shigar a babbar kotun jiha kan batun zabtare musu albashi da gwamnati ta yi amma gwamnatin za t ayi biyayya da hukuncin Kotun”. A cewar Barista Lawan Abdullahi Musa.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa Barista Lawan Abdullahi na cewa, gwamnatin Kano ta sauyawa kamfanin buga jarida na TRIUMPH guri zuwa rukunin gidaje na Shekh Isyaka Rabiu domin cigaba da gudanarda ayyukansu a can.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Ina zargin mai sayar da fili ya bani takardar Biredi – Wata Mata

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu, wata mata ta yi karar wani mutum da cinye mata Filaye guda takwas ta hanyar ba ta takardun bogi.

Sai dai kafin fara shar’ar ne kotun ta samu sanarwar dakatar da gudanar da shari’a saboda hutu da kotunan jihar Kano su ka tafi a ranar ta Talata.

Saurari wannan domin jin cikakken rahoton.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotunan jihar Kano na jiran umarnin tafiya hutu a rubuce – Baba Jibo

Published

on

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya tabbatar da umarnin rufe kotunan jihar Kano a ranar Talata.

Sai dai Baba Jibo Ibrahim a yayin zantawarsa da wakilin Ibrahim Abdullah Sorondinki ya ce, suna jiran umarnin ne a rubuce domin sanar da kotuna da kuma sauran al’umma akan halin da ake ciki.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: ‘Yar kasuwa ta gurfana a kotu kan zargin cinye manyan Kudade

Published

on

Babbar kotun shari’ar musulunci da ke filin Hockey karkashin mai shari’a Abdullahi Halliru Abubakar, ta gurfanar da wata mata kan zargin karbar kudi Naira miliyan tara da dubu dari shida a hannun wani mutum da zummar za su yi harkar kasuwancin Dala.

Mutumin mai suna Musa Yusuf Abubakar yana karar matar mai suna Farida Usman Dantata, da cinye kudaden, wanda kuma kasancewar ranar Talatar hutu a ke yi mai shari’a bai zo ba, aka dage shari’ar zuwa ranar biyu ga watan uku shekarar 2021.

Domin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!