Ilimi
Rahoto: Zanga-zanga mu ka yi ba yajin aiki ba – BUK

Ma’aikatan jami’ar Bayero a jihar Kano, sun kasance a cikin jerin ma’aikatan jami’o’in Nijeriya a kan wata zanga-zangar lumana da su ka gudanar a safiyar ranar Talata.
Gamayyar manyan ma’aikatan da kanana na SANU da kuma NASU ne su ka gudanar da Zanga-zangar a harabar sabuwar jami’ar Bayeron a jihar Kano.
Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya halarci wajen zanga-zangar ya aiko mana rahoto daga jami’ar.
Ilimi
Adaidaita Sahu: An samu karancin fitowar dalibai da malamai a makarantun Kano

Makarantu a jihar kano sun fuskanci karancin dalibai da malamai, sakamakon yajin aikin direbobin Adaidaita Sahu suka shiga.
A zagayen da gidan rediyon Dala ya gudanar da safiyar yau Litinin zuwa wasu makarantu, mun tarar har zuwa karfe Goma na safe da yawa daga cikin makarantun babu dalibai da malamai sai ‘yan kalilan, harma a zantawar mu da wata shugabar makarantar firamare ta ce itama sai karfe Tara saura ta samu zuwa makarantar, sabo da rashin abun hawa na Adaidaita Sahu, domin haka yau ko asambile ma basu samu damar yi ba dukda cewar yau Litinin.
Wakilin mu, Ibarahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa tasgaron da yajin aikin na matuka baburan Adaidaita Sahu ya kawo, ya kuma shafi harkokin kasuwanci da ayyuka a hukumomi da ma’aikatun gwamnati da masu zaman kan su daban-daban, sakamakon rashin zuwan ma’aikatan a kan lokaci ko kuma rashin zuwan na su ma baki daya.
Ilimi
Adaidaita Sahu: Yajin aikin ya shafi daliban mu na jeka ka dawo – KSSSMB

Hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar Kano ta ce yajin aikin da aka shiga ya shafi daliban ta na jeka ka dawo duk da cewa harka ta koyo da koyar w aba ta tsaya ba a fadin jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Baba Musa ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala a safiyar yau Litinin.
Ya ce,”Mu na fatan wannan abun da aka shiga za a samu daidaito, domin dalibai su koma bakin aiki yadda ya kamata. Kuma batun lalacewar wasu motocin daukar dalbai a Kano, daman dole ne a samu wasu sun lalace saboda zirga-zirgar yau da kulum, amma kuma wasu sun yi aiki a safiyar Litinin dinnan sun kwashi dalibai sosai, sauran kuma za a yi kokari wajen ganin gwamnati ta gyara motocin daukar daliban da su ka lalace”.
Ilimi
Motocin Kurkura sun kaiwa dalibai dauki ciki harda motar daukar marasa lafiya

Motocin kurkura masu dakon kaya sun taka gagarumar gudunmawa wajen kaiwa dalibai dauki ciki harda motar daukar marasa lafiya wato Ambulance, sakamakon yajin aiki da masu baburan Adaidaita sahu suka daka a safiyar Litinin dinnan.
Wakilin mu na ‘yan ZAZU, Tijjani Adamu ya hangi irin yadda masu motocin kurkuna suka rinka dibar fasinja ciki harda daliban makarantun Firamare da na sakandire da kuma nag aba da sakandire.
Haka zalika wakilin namu ya kuma tarar da wata motar daukar marasa lafiya na kokarin sauke daliban Firamare da aka kawo su bakin makarantar su a cikin kwaryar birni.
Wannan ya biyo bayan rashin jituwar da aka samu tsakanin direbobin Adaidaita sahu da kuma hukumar KAROTA.
-
Manyan Labarai1 year ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi1 year ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai12 months ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi1 year ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 months ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi1 year ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai1 year ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari
-
Manyan Labarai1 year ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano