Labarai
Sojan gona: An fara sauraron shari’ar lauyan bogi
Alkalin babbar kotun shari’ar Musulinci dake Kofar Kudu Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya fara sauraron karar wani matashi da ake zargi da laifin sojan gona a aikin lauyane.
Wanda ake zargin mai suna Isa Muhd ana tuhumarsa ne da laifin yin sojan gona ga alkalin wata babbar kotun shari’ar Musulinci tare da bayyana kan sa cewa shi lauyane harma ya nemi alfarmar kotu ta dage sauraron wata karar gado dake gaban kotun.
Daga bisani asalin wadanda suka shigar da kara a kotun suka shaidawa alkali cewa ba lauyansu bane yasa aka dage karar hakan yasa alkali ya bada umarni akamo Isa bayan an kama shi kuma ya tabbatarda cewa shi ba lauya bane.
A zaman kotun na yau Sarki Yola ya saurari shaidar masu kara inda Nazifi ya bada shaidar abunda ya faru akan idonsa a gaban alkalin kotun a ranar sha biyu ga watan takwas na shekarar data gabata.
Wakilin mu Abdulkarim Muhd Tukuntawa ya rawaito mai sharia Sarki Yola ya sanya ranar tara ga watan uku a matsayin ranar da za’a cigaba da sauraron karar.
Labarai
Shugabanni ku fito da sabbin dabaru domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta tsadar rayuwa a ƙasa – Human Rights
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights dake jihar Kano, ta ce akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya dace dan ganin an kawo karshen matsalar tsaro, da kuma ta harkar tsaro dake ci gaba da addabar mutane a sassa ƙasar nan.
Daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Laraba, ya ce yadda ake ƙara samun ƴan ta’adda suna sace mutane tare da kashe su a sassan ƙasar nan, da kuma halin matsin rayuwar da ake fuskanta akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya kamata dan ganin an kawo ƙarshen matsalolin.
“Yawaitar kai hare-haren da ake samu daga ɓangaren ƴan bindiga a cikin al’ummar gari akan kashe su tare da sace su matuƙar ana son a kawo karshen matsalar, sai an ƙara himma wajen samar da makamai ga jami’an tsaro tare da samar da sabbin dabaru domin kawar da matsalar, “in ji Galadanci”.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan da sako ɗalibai aƙalla su sama da 285, na makarantar Kuriga dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, da ƴan bindiga suka sace su a baya, baya ga wasu ɗaliban da aka sace a wata makarantar Tsangaya a jihar ta Kaduna, wanda ko a jihar Borno ma aka jiyo yadda aka sace ƴan gudun hijira da dama a baya-bayan nan, inda matsalolin tsaron ke ƙara yin gaba a sassan ƙasar nan.
Labarai
Gwamnan Kano ya kafa kwamitin duba yadda ake rabon tallafin abincin Azumi
Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin duba yadda ake ciyarwar azumin watan Ramadan, a kananan hokumomin cikin birnin jihar 8, domin sa ido da duba yadda ake gudanar da aikin dafawa da rabawa al’umma abincin.
Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin ne ƙarƙashin kulawar mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da wasu ƴan kwamitin.
Hakan na zuwa ne dai bayan da gwamna Abba Kabir, ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da ake dafa abincin, inda ya nuna rashin jin daɗin sa kan yadda ya ga aikin ke gudana a karamar hukumar kumbotso.
Bayanin hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwar da babban mai taimakawa gwamnan Kano, na musamman akan gidajen rediyo Bashir Aminu Fanshekara, ya aikowa manema labarai, ya ce an bayyana Alhaji Danyaro Yakasai, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin mai mambobi 7.
Fanshekara ya ce kwamitin ya fara zagayawa wasu daga cikin mazaɓu dake karamar hukumar kumbotso, domin duba yadda ake dafawa da kuma raba abincin tallafin ga al’umma, inda suka suka fara da mazaɓar Na’ibawa a ranar Asabar 23 ga watan Maris ɗin shekarar 2024.
Ilimi
Kaduna:- Daliban Kuriga sun sha ki iskar ‘yanci
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da rahoton cewa an sako duka ɗaliban makarantar Kuriga da ƴanbindiga suka sace.
An sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna fiye da makonni biyu da suka wuce.
Sanarwar da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fitar ta ce an sako duka ɗaliban kuma suna cikin koshin lafiya.
Sanarwar ba tayi karin bayani ba game da irin matakan da aka bi wajen sako ɗaliban, sai dai gwamna Uba Sani ya nuna godiya ga shugaba Tinubu da mai bashi shawara kan tsaro da kuma sojojin Najeriya saboda irin rawar da suka taka wajen ganin an sako ɗaliban.
“Ba dare babu rana ina tattaunawa da Malam Nuhu Ribadu domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kubutar da daliban, kafin mu samu nasara,” in ji Uba Sani.
Galibinsu ɗaliban da aka sace ƴan shekaru biyar ne zuwa 18.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su