Wasanni
Wasan Golf: Na lashe kofi da dama a wasan – Sule Imam Daura

Wani dan wasan kwallon Golf, a jihar Kano, Sule Imam Daura, ya ce ya lashe kofi da dama a wasan a iya tsawon lokacin da ya fafata a wasan.
Ya ce wasan na motsa jiki ne ba wai iya lashe kofin ba kadai, domin kuwa har ta kai sai da gabobin jikin shi su ka koma daidai sabanin a baya.
Daga filin wasan kwallon Golf na Kano Club, wakilin mu Musa Abdu Tudun Wada ya turo mana da rahoto.
Wasanni
Wasan Golf: Yadda matasa su ka karbi wasan Golf a Kano

Wasu matasa a jihar Kano da suke wasan kwallon Golf sun ce a yanzu haka sun karbi wasan Golf a matsayin wasan da za su nuna bajinta a cikin kwallon Golf.
Daga filin wasan kwallon Golf na Kano Club wakilin mu Musa Abdu Tudun Wada ya turo mana da rahoto.
Wasanni
Division 2: Sakamakon gasar a Kano

Sakamakon gasar Division 2 da ake fafatawa a jihar Kano.
Affar Utd ta doke Fc Mai Kwai da ci 1-0
Jarma Fagge – 2 All Star Yan kaba- 1
Fc Milo – 0 Dan Dalama – 3
Mujan Warriors – 2 Fc Yelwa – 0
Mabusa Fc – 1 Blue Star Unguwa Uku – 2
Jakada Utd – 1 Ajingi Unted – 0
Golden Star Bunkure – 3 Junior Highlanders – 2.
Wasanni
Kano: Gasar Unity Cup da Divison Two

A gasar cin kofin Unity na kakar 2020 da 2021 da ake fafatawa a jihar Kano.
Kungyar kwallon kafa ta Zoo United ta yi rashin nasara da ci biyu da nema a hannun Super Star Sheka. Dan wasa Nasiru Shamalala shine ya jefa kwallon farko minti 21 yayin da Babu Messi ya jefa kwallo ta biyu 79.
A wasan sada zumunci da za a fafata a yammacin Juma’a.
Kungiyar kwallon kafa ta FC Rising Stars za ta barje gumi da New Stars FC
A filin wasa na New Star.
Mazugal United za ta karbi bakwancin FC Kofar Ruwa a filin wasa na Kofar Mazugal filin Holo.
ita kuwa FC Sharifai Academy kece raini za ta yi da Ahmad Academy a yammacin ranar Lahadi a filin wasa na Ramcy dake kwalejin Rumfa.
A gasar cin kofin ajin matasa na rukuni na daya wato Divison One cikin rukuni na 8 da za a fafata a yammacin gobe.
Old Star Dawakin Kudu da FC KAROTA a filin wasa na biyu dake Mahaha.
Gaida United za ta kara da Tango United a filin wasa na Kano United dake Mahaha.
ADS FC za ta kece raini da Zage United a filin wasa na Sharada United dake Mahaha.
A rukuni na 9 kuwa a cikin gasar, Dala United da Kurna FC a filin wasa na Sagagi dake Mahaha.
National Star Dukawa za ta gwada kwanji da Super Real a filin wasa na Diso United dake Mahaha.
A yayin da Fantel FC za ta kara da Junior Pillars ‘yan kasa da shekaru 15 a filin wasa na hudu dake Mahaha.
-
Manyan Labarai11 months ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi1 year ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai11 months ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi1 year ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai12 months ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari
-
Nishadi1 year ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Labarai3 months ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai12 months ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
You must be logged in to post a comment Login
You must log in to post a comment.