Connect with us

Wasanni

Unity Cup: Yadda sakamakon gasar ke wakana a Kano

Published

on

Samba Kurna FC 2- 1 Asosa Kurna FC

Tahir FC 2- 2 Sky Tawayya FC

Leaders FC 3- 1 Kano United

A gasar kofin Habu PA.

Gyadi Gyadi Arewa 5 Unguwa Uku kauyen Alu 4 bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan anyi kunnen doki 2-2.

 

Wasanni

Kwallon Golf: Da na sani tun farko wasan Golf na fara maimakon kwallon kafa – Birniwa

Published

on

Dan wasan kwallon sandan Golf, Haruna Abubakar Birniwa, ya ce tun da aka koya masa wasa ya kware ba tare da jimawa ba, har ta kai ya samu nasara cikin kalilan lokaci.

Dan wasan Haruna Birniwa, ya kuma ce da farko ya fara wasan kwallon kafa wanda har kasar Turai ya je ya taka leda daga baya kuma ya sauya sheka zuwa wasan kwallon sandan Golf.

Daga filin wasan kwallon Golf, wakilin mu Musa Abdu Tudun Wada ya turo mana da rahotan shi.

Continue Reading

Wasanni

Wasan Dambe: Shagon Maye ya yi kisa a dakika 27

Published

on

A gidan wasan Damben gargajiya dake Ado Bayero Square a Unguwar Sabon Gari a jihar Kano kuwa, an Dambata ne tsakanin Arewa da Kudu sakamakon babu wanda ya daure hannu daga bangaren Gurumada.

Cikin rukunin ajin manyan ‘yan Dambe an fara fafatawa ne tsakanin Shagon Dan Bature na Arewa da Dan Sama’ila Shagon Alabo na Kudu saidai wasan babu nasarar kisa.

Shagon Maye ya kashe Shagon Shattima dakika 27 da hura wasan.

Dogon Zee Y ya buge Rabe Bahagon Ebola a turmin farko.

Shagon Garkuwar Bahagon Musa da Coronavirus ba kisa.

Na Master Ali ya kashe Dadan Kwalawa a turmi na biyu.

Dogo na Karkarna ya buge Shagon Mada a turmi na biyu, kamar yadda wakiliyar mu a fagen Damben Hadiza Jinta ta rawaito.

Continue Reading

Wasanni

Kano Pillars: Baleria ya cika shekara guda da mutuwa

Published

on

A irin wannan rana ta Alhamis 25 ga watan Fabrairu na shekarar 2020, tsohon Manajan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Marigayi Kabiru Baleria ya cika shekara guda cif da rasuwa.

Marigayi Baleria ya rasu ne a ranar 25 ga watan Fabrairu, sakamakon rashin lafiya.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!