Wasanni
Continue Mandawari ta sayar da‘yan wasa biyu a kan Naira dubu 20

Kungyar kwallon kafa ta Continue Mandawari ta sayar da ‘yan wasa guda biyu daga kungiyar kwallon kafa ta Manadawari Itihad.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafin sada zumunta na Coach’s Forum Dala FM wanda mataimakin shugaban kungiyar Sani Baban Iya Mandawari ya fitar.
Sanarwar ta ce kungiyar ta Continue Mandawari ta sayar da wasa Musa Abdullahi Kwali da kuma Abdullahi Aminu Huntler.
Mataimakin shugaban kungiyar, Sani Baban Iya ya ce an cimma yarjejeniya da kungiyoyin biyu a kan kudi Naira dubu ashirin dukannin ‘yan wasan.
A ranar 25 ga watannan kungiyar za ta fafata da ‘yan wasan tawagar Sirrin Zuciya da kuma Good Friends na murnar dan wasan su bisa baiko da a ka yi masa.
Wasanni
Unity Cup: Sakamakon wasan da a ka fafata

M.Y Jameel 0-0 ZOO United
Soccer Strikers 2-2 Clever Warriors
Kano Rovers 2-1 Gama Emirates
Dabo Babies 1-1 Samba Kurna
Wasanni
Muntari Pro ya zama mai horaswa na Kano Municipal

Shugaban karamar hukumar Birni da kewaye, Fa’izu Alfindiki, ya nada Muntari Ado Dan Dolo wato Muntari Pro a matsayin sabon mai horaswa nakungiyar kwallon kafa ta Kano Municipal.
Yanzu haka Muntari Pro zai jagoranci tawagar kungiyar, har nan da zuwa wasu lokutan a matsayin sabon mai horaswa.
Wasanni
Shining Star Dorayi ta kori masu horaswa tare da daukar dogon hutu

Kungiyar kwallon kafa ta Shining Star Dorayi, ta sallami masu horaswar ta Auwalu Maye da kuma Usman Dankalat tare da Halilu Duniya.
Cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar, Barrista Aminu Usman ya fitar ta shafin sada zumunta na masu horaswa da shugabannin kungiyoyi na Dala FM a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce sakamakon wasu abubuwa da suka faru a gasar Tofa Division One mai taken Ahlan Cup, ya sanya kungiyar ta yanke wannan hukunci.
Kungiyar ta kuma ce yanzu haka ta dakatar da daukar horo har sai bayan karamar Sallah, sannan za ta dawo ta ci gaba da yin atisaye.
Haka zalika sanarwar ta ci gaba da cewa, kungiyar ta baiwa dukkanin ‘yan wasan ta hutu har sai nan da wani lokaci, kuma idan za ta dawo za bayyana irin ‘yan wasa da masu horaswar da ta ke bukata, sannan duk wanda ba ta kirashi ba, zai iya canja kungiya. Ta kuma ce yanzu haka ta yanke shawarar wakiltat yankin Dorayi dake karamar hukumar Gwale.
Yau kimanin watanni biyu kenan da yi wa kungiyar garanbawul, ciki harda masu horaswar da ta sallama wanda a baya ta daga likafar su, a yanzu kuma ta sallame su baki daya.
-
Manyan Labarai1 year ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi1 year ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai1 year ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi1 year ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai5 months ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi1 year ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai1 year ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari
-
Manyan Labarai1 year ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano