Connect with us

Labarai

Rundunar ‘yan sanda ta yi holin wadanda ake zargi da garkuwa da mutane a Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi holin mutane hudu wadanda ta kama kan zargin garkuwa da mutane a Kano a unguwar Jaba dake karamar hukumar Ungogo.

Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin holing wadanda ake zargi.

Ya ce, sunyi musayar wuta da jami’an tsaro da wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane lokacinda suka je kama su.

Ya kuma ce, wadanda ake zargin sun hada da Maryam Muhammad yar shekaru 23 sai Sani Ibrahim da kuma Shamsu Sulaiman ‘yan asalin jihar Zamfara da kuma Ishaq Khalil wanda aka fi sani da Baban Basma dake jihar Kano.

Wakilin mu Abdulkarim Muhd Tukuntawa ya rawaito cewa, an samu alburusai masu yawan gaske da kuma bindiga kirar AK 47 a wajen ‘yan garkuwar.

Labarai

Hana maza shiga gidan aure: Za a koyawa mata aikin gyaran famfo da wutar lantarki

Published

on

Gwamnatin jihar Kano za ta kashe Nara miliyan dubu biyu, domin koyar da mata yadda za su yi aikin gyaran wutar lantarki da gyaran famfo.

Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi a jihar Kano, Murtala Sule Garo ne ya bayyana haka, yayin kaddamar da rabon tallafi na Naira dubu goma-goma ga mutane 1000 a karamar hukumar Takai.

Murtala Sule Garo ya ce”Abun takaici ne a ce jihar Kano da ta ke koyi da musulunci a ce idan wata matsala ta faru a cikin gida sai namiji ya shiga gidan matan aure sannan za a iya magance ta”.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara da ta halarci taron ta rawaito mana cewa, mata da dama ne za su ci gajiyar koyon aikin gyaran wutar lantarki da na famfo domin kawo karshen shigar maza cikin gidaje mata.

Continue Reading

Labarai

A samar mana da makarantar kiwo lafiya da sakandire – Shugaban karamar hukumar Takai

Published

on

Shugaban karamar hukumar Takai kuma shugaban shuwagannin kananan hukumomi, Muhammad Baffa ya roki gwamnatin jihar Kano da ta samar da makarantar kiwon lafiya da asibiti da kuma makarantar sakandire a yankin Takai.

Bayanin hakan na zuwa ne ya yin kaddamar da rabon tallafin Naira dubu goma-goma wanda mutane dubu guda za su amfana a karamar hukumar.

Muhammad Baffa ya ce”Kasancewar babu makarantar gaba da sakandire a karamar hukumar ya na kawo koma baya a cigaban karatun ‘ya’yan mu”.

Continue Reading

Labarai

Rashin sana’a: Samari su guji kashewa ‘yan mata kudi – Hafsa Abdullahi Umar Ganduje

Published

on

Mai dakin gwamnan Kano, Hajiya Hafsa Abdullahi Umar Ganduje ta gargadi matasa da su gujewa kashewa ‘yan mata kudi matukar basu da tsayayyar sana’ar da za su aure su.

Hajiya Hafsa Ganduje ta yi wannan gargadin ne yayi rabon jari ga mata 600 da matasa 400 a karamar hukumar Takai a ranar Asabar.

Ta ce”Matasan da su guji baiwa mata kudin da a ka basu, domin idan su ka juya kudin za su sami abun da za su dogara da kan su har su aure ‘yan mata”.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara, ta rawaito mana cewa Hajya Hafsa Abdullahi Umar Ganduje ta tabbatar da cewa za ta yi duk mai yuwa wajen ganin an inganta asibitin garin da kuma samar da makarantar kiwon lafiya a karamar hukumar Takai.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!