Connect with us

Labarai

Hukumar KAROTA ta kama Tabar Wiwi ta Naira Miliyan 30

Published

on

Hukumar da ke kula da ababen hawa a jihar Kano, KAROTA ta kama wata mota kirar Golf dake dauke da buhunan tabar Wiwi zuwa jihar.

Hakan na cikin wata takarda mai dauke da sa hannu Kakakin hukumar, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa aka raba manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, an kama  motar ne da misalin karfe uku da rabi na daren Laraba akan hanyar Gwarzo yayin da sauran wadanda ake zargin masu kayan ne suka samu damar tserewa.

Bincike na farko ya nuna an samu jimillar kunshin tabar Wiwi 172 wadda ta kai Naira Miliyan 30, inda hukumar ta KAROTA ta mika kayayyakin ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA don ci gaba da bincike.

Shugaban hukumar ta KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi ya sake yin kira ga jama’a da su taimaka wa hukumar da ingantattun bayanai da za su kai ga kame duk wani mutum ko gungun wasu mutane da ke aikata kowane irin laifi a cikin jihar musamman a kan hanyoyin jihar.

Labarai

Babu buƙatar shirya zaman muƙabala da Malam Abaduljabbar – Sarkin musulmai

Published

on

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce, babu buƙatar shirya wani zaman muƙabala tare da Malam Abaduljabbar Nasiru Kabara.

Sarkin ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam da ya ke shugabanta ta fitar ta hannun babban sakataren ta Dr. Khalid Abubakar Aliyu.

Sanarwar ta ce, a baya ta yaba wa Gwamnatin Kano dangane da matakin da ta ɗauka na dakatar da Malam Abduljabbar Kabara daga karatu tare da rufe masallacinsa, la’akari da kalaman malamin to babu buƙatar shirya wani zaman muƙabala tare da shi.

A ƙarshe JNI ta ce, ita da mambobinta sun cimma matsaya a kan ba za su shiga duk wani taro da aka shirya domin tattauna wa da malamin ba, kuma tana fata Gwamnatin Kano za ta yi la’akari da wannan matsaya da ta ɗauka domin sauya matsaya.

A ranar Lahadi ne Gwamnatin Kano ta shirya gabatar da wannan muƙabala da ta ce, Mai Alfarma Sarkin Musulmi zai zamo babban baƙo.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Al’ummar Sharaɗa sun shiga fargaba saboda jin karar harbe-harbe

Published

on

Al’ummar yankin Sharada yankin NNDC, sun shiga cikin fargaba yayin da su ka ji karar harbe-harben bindiga a daren Talata.


A lokacin da mutanen unguwar suka leko sun ga wani makwabcin su da bindiga ya na ta faman harbi a sararin sama da sanyin safe kuma ya fito ya na tsintar kwansar harsashen.


Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a kan lamarin sai dai har yanzu bai magantu ba a kan zancen.


Saurari wannan domin jin cikakken rahoton.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Ma’aikatan jinya su kare kan su a kan Corona – Kungiyar ma’aikatan jinya

Published

on

Kungiyar ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta kasa reshen jihar Kano, ta bukaci ma’aikatan Jinya da Ungozoma da su ci gaba da kulawa da kan su yayin jinyar masu dauke da cutar Corona.


Shugaban kungiyar reshen jihar Kano, Kwamared Ibrahim Mai Karfi ne ya gargadi ma’aikatan yayin da kungiyar ta kai ziyara ma’aikatar lafiya ta jihar Kano a ranar Laraba.


Ya kuma ce, “Kamata ya yi idan al’umma sun ji yanayin su ya sauya, su yi kokarin tuntubar masana lafiya maimakon su je su sayi magani kai tsaye su sha”.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!