Connect with us

Wasanni

Na fara wasan Golf da daukar jakar ‘yan wasa – Adamu Sa’idu

Published

on

Wani jamii’in daura dammara a Nijeriya kuma kwararre a harkar kwallon Golf, Adamu Sa’idu, ya ce ya fara wasan ne da dakwan jakar zakakuran ‘yan a harkar, har shima ya samu damar zama zakara a wasan.

Adamu Sa’idu ya ce ya samu Zinarya da Azurfa na gasar kwallon Golf na ‘yan sanda da dai sauran su. Ya kuma yi kira ga matasa cewa ka da su zama cima zaune su shigo a fafata da su.

Musa Abdu Tudun Wada daga filin wasa na kwallon Golf dake Kano Club, ya hada mana rahoto.

 

Wasanni

Unity Cup: Sakamakon wasan da a ka fafata

Published

on

M.Y Jameel 0-0 ZOO United

Soccer Strikers 2-2 Clever Warriors

Kano Rovers 2-1 Gama Emirates

Dabo Babies 1-1 Samba Kurna

Continue Reading

Wasanni

Muntari Pro ya zama mai horaswa na Kano Municipal

Published

on

Shugaban karamar hukumar Birni da kewaye, Fa’izu Alfindiki, ya nada Muntari Ado Dan Dolo wato Muntari Pro a matsayin sabon mai horaswa nakungiyar kwallon kafa ta Kano Municipal.

Yanzu haka Muntari Pro zai jagoranci tawagar kungiyar, har nan da zuwa wasu lokutan a matsayin sabon mai horaswa.

Continue Reading

Wasanni

Shining Star Dorayi ta kori masu horaswa tare da daukar dogon hutu

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Shining Star Dorayi, ta sallami masu horaswar ta Auwalu Maye da kuma Usman Dankalat tare da Halilu Duniya.

Cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar, Barrista Aminu Usman ya fitar ta shafin sada zumunta na masu horaswa da shugabannin kungiyoyi na Dala FM a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce sakamakon wasu abubuwa da suka faru a gasar Tofa Division One mai taken Ahlan Cup, ya sanya kungiyar ta yanke wannan hukunci.

Kungiyar ta kuma ce yanzu haka ta dakatar da daukar horo har sai bayan karamar Sallah, sannan za ta dawo ta ci gaba da yin atisaye.

Haka zalika sanarwar ta ci gaba da cewa, kungiyar ta baiwa dukkanin ‘yan wasan ta hutu har sai nan da wani lokaci, kuma  idan za ta dawo za bayyana irin ‘yan wasa da masu horaswar da ta ke bukata, sannan duk wanda ba ta kirashi ba, zai iya canja kungiya. Ta kuma ce yanzu haka ta yanke shawarar wakiltat yankin Dorayi dake karamar hukumar Gwale.

Yau kimanin watanni biyu kenan da yi wa kungiyar garanbawul, ciki harda masu horaswar da ta sallama wanda a baya ta daga likafar su, a yanzu kuma ta sallame su baki daya.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!