Connect with us

Ilimi

Yara su dage da karatun addini a Kano – Sarkin Kano

Published

on

Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gargaɗi daliban makarantun Islamiyya da su ƙara ƙaimi wajen neman ilmin addinin musulunci, domin rabauta da rahmar Allah (S.W.T) a nan duniya dama ranar gobe ƙiyama.

Alhaji Aminu Ado ya bayyana hakan ne a yayin saukar karatun Alkur’ani mai girma, da makarantar Madarasatul Ta’alimul Kur’an Waddarasatul Qur’an ta gudanar a unguwar Sheka daura da Tudun Maliki dake yankin ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Ya na mai cewa,”Matuƙar ƴara suka tashi tsaye wajen neman ilimin addinin musulunci da na zamani, babu shakka za a samu raguwar lalacewar tarbiyyar su da a kan samu a wannan zamani”. A cewar Sarkin Kano.

Da yake nasa jawabin shugaban makarantar Mallam Muhammad Nura Idris, miƙa godiyar shi ya yi ga dukkanin ilahirin al’ummar da suka halarci saukar karatun Alkur’anin mai girma, musamman ma Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.

Ita ma ɗaya daga cikin tsofaffin Ɗaliban makarantar, kuma shugabar sashin addinin musulunci ta gidan rediyon Dala FM Kano, Malama Hadiza Balanti, ta yabawa malaman makarantar tare kuma da kira ga ɗaliban da su ka yi saukar da su ƙara himmatuwa wajen kulawa da karatun su.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’unya rawaito cewa, kimanin Ɗalibai 26 ne su ka yi Saukar Karatun Alkur’anin mai girma.

Ilimi

Hukumar Hisba su faɗaɗa aikin su zuwa gidajen wasanni a watan Ramadan – Dr Abdullah

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Usman Bin Affan dake unguwar Gadon Ƙaya, Dakta Abdallah Usman Umar, ya shawarci gwamnatin Kano da ta ƙara duƙufa wajen samarwa da hukumar Hisbah motoci da kayan aiki, domin ƙara samun damar hidimtawa addinin musulunci.

Dakta Abdallah ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Rayuwa Abar Koyi na Dala FM Kano, wanda ya gudana da ƙarfe tara zuwa goma na safiyar Juma’a.

Ya na mai cewa,”Siyawa hukumar Hisbar motoci da kuma kayan aiki, zai taimaka musu matuƙa musamman ma wajen daƙile alfasha a watan da yake kara gabatowa na Azumi dama sauran watannin baki ɗaya, domin ƙin bawa hukumomin da suke taimakawa addini da al’umma yakan ƙara haifar da saɓo, su kuma hukumar Hisbar su faɗaɗa aikin su zuwa gidajen wasanni, domin daƙile ɓarna da take gudana”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Dakta Abdallah Usman Umar, ya kuma shawarci mutanen da azumi ya wajabta a kan su suke ƙin yi, da su tuba su daina hakan, domin gudun fishin Allah (S.W.T).

Continue Reading

Ilimi

Malaman makarantun gwamnati ku kara zage damtse a kan aikin ku – Hafsat Ganduje

Published

on

Matar gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta nemi Malaman makarantu cewa su kara jajircewa wajen yin aiki a kan irin dabarun koyo da koyarwan da su ka samu.

Farfesa Hafsat Ganduje ta yi kiran ne lokacin da a ke taron a kan fannin ilimi da ya wakana a jami’ar Bayero.

Farfesa Hafsat Ganduje ta kuma yabawa gwamnatin jihar Kano bisa yadda ta baiwa bangaren Ilimi kaso 26 a cikin kasafin kudin shekarar nan.

Continue Reading

Ilimi

Ilimi kyauta: Yawan dalibai a makarantun Firamari ya karu a Kano – Danlami Hayyo

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce sakamakon ilimi kyauta kuma dole a makarantun Firamare a jihar, yawan dalibai ya karu zuwa miliyan uku da dubu dari takwas, maimakon dalibai miliyan daya da dubu dari biyar a baya.

Shugaban hukumar ilimin bai daya a jihar Kano, Dakta Danlami Hayyo ne ya bayyana hakan yayin taron kungiyar kwararru a fannin ilimi da gudanarwa da kuma tsare-tsare wanda ya gudana a jami’ar Bayero karo na biyar.

Danlami Hayyo ya ce”Gwamnatin jihar Kano ba ta yi kasa a gwiwa ba koda lokacin cutar Corona, domin kuwa ta na koyar da darusa a kakafafen yada labarai, wanda wasu jihohin su ka yi koyi da ita”.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!