Connect with us

Labarai

Masarutar Karaye ta nada Kwankwaso a matsayin Makaman Karaye

Published

on

Mai martaba Sarkin Karaye, Alhaji Dr Ibrahim Abubakar na II ya nada Alhaji Saleh Musa Saleh Kwankwaso a matsayin Makaman Karaye hakiman gundumar Madobi tare da wasu hakimai guda hudu.

Sauran hakiman da akwai Alhaji Ibrahim Sani Gaya a matsayin Sarkin Shanun Karaye hakimin Shanono kuma Dan majalisar Sarki da Alhaji Sidi Mustapha Karaye a matsayin Dan masanin Karaye kuma Dan majalisar Sarki. Yayin da a ka nada Alhaji Bashir Mai kudi Aminu da Alhaji Ahmad Muhammad Tudun Kaya a mukaman San Turaki da Shattiman Karaye.

Kafin nada sabon Makaman na Karaye har ila yau Danmajalisar Sarki kuma daya daga cikin masu zabar Sarki na masarautar ta Karaye.

Da yake jawabi yayin nadin, Mai Martaba Sarkin Karaye Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II ya ce“Ku kasance masu biyayya da kuma ci gaba da bada gudunmawa domin tabbatar da ci gaban masarautar”.

Cikin sanarwar da Haruna Gunduwawa wanda shi ne babban Jami’ in yada labarai na masarautar Karaye ya sanyawa hannu ta ce mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna tare da tawagar gwamnatin jihar Kano ne suka samu damar halartar taron nadin.

Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II ya kuma godewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa kokarin shi na samar da managarciyar ruyuwa al’ umma. Sannan ya kuma sake jaddada bukatar shi ga Gwamnatin da ta gaggauta kammala aikin hanyar da ta shi daga Janguza ta tafi Kabo ta kuma zarce Karaye, domin amfanin al’ummar Masarautar.

Dr. Ibrahim Abubakar II ya ce”Wannan hanya na da makukar amfani wajen habaka tattalin arzikin al’ummar yanki, kuma ita ce hanya mafi sauri wajen zuwa birnin Kano daga Karaye”.

 

Labarai

Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.

Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.

Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.

Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.

Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.

Continue Reading

Labarai

Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.

Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.

Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.

Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!