Connect with us

Manyan Labarai

KASASHEN SUDAN DA LIBYA DA CHADI DA KUMA NIJAR SUN CI ALWASHIN HADIN GWIWA A TSAKANIN JUNA DON KALUBALANTAR HARKOKIN TSARO AKAN IYAKOKIN SU

Published

on

Kasashen Sudan da Libya da Chadi da kuma Nijar sun ci alwashin hadin gwiwa a tsakanin juna don kalubalantar harkokin tsaro akan iyakokin su tare da magance ta’addanci da sauran manyan laiffukan dake faruwa akan iyakokin su.
Minstan harkokin wajen kasar Sudan Al-Diriri Muhammad Ahmad ne ya bayyana hakan yayin taron ministocin kasashen karo na uku da ya gudana jiya Alhamis a birnin Khartoum na kasar Sudan.
Yace nasarar da darakrun kasashen Sudan da Chadi suka samu na tabbatar da tsaro akan iyakokin kasashen biyu, ya nuna irin nasarar da aikin hadin gwiwar zai haifar.
A nasa jawabin, Ministan tsaro na jamhuriyar Nijar, Kalla Mountari, kira yi da a hanzarta tsara matakan hadin giwar tabbatar da tsaron a kan iyakokin kasashen, musamman ta hanyar bullo da dabarun musayar muhimman bayanai kan tsaron iyaka, duba da irin kalubalen da kasashen yankin ke fuskanta.
A watan Yunin da ya gabata ne kasashen hudu suka sanya hannu kan wata yarjejeniya a birnin N’Djamenan kasar Chadi, game da yadda za a tabbatar da tsaro da sa ido akan iyakokin kasashen.
Yarjejeniyar ta amince a rinka gudanar da sintiri na hadin gwiwa akan iyakokin kasashen, da musayar muhimman bayanai, da kafa cibiyar ayyukan hadin gwiwa da kuma aiwatar da ayyukan raya kasa a kan iyakokin kasashen hudu.

Manyan Labarai

Ƙarancin wutar lantarki na bamu matsala a asibitocin Kano – Dr. Mansur Nagoda

Published

on

Hukumar dake kula da asibitoci ta jihar Kano, ta ce zafin da ake fama dashi a yanzu, da kuma ɗaukar zafin injinan su bisa yanayin rashin wutar lantarki, shi dalilin da ya sa ake samun matsala, wajan bada kulawa ga mata masu haihuwa, da waɗanda za’a yiwa Tiyata a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke jihar.

Shugaban hukumar dake kula da asibitocin ta jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda ne ya bayyana wa gidan Rediyon Dala FM, hakan a ranar Asabar.

Nagoda, ya kuma ce a mafi yawan lokuta idan aka shiga da mutum Tiyata, musamman ma mace aka fito da ita ba’ayi ba, haka na da nasaba ne da rashin lafiya, ko kuma ba zata iya ɗaukar iskar baccin da ake bayarwa ba.

A cewar sa, “Da yawan mutane basa yi mana uzuri game da halin da ake ciki na rashin wutar lantarki duk da kasancewar suna zagaya asibitoci, domin tabbatar da marasa lafiya sun samu kulawar data dace, “inji Nagoda”.

Ya kuma ce bangaren duba lafiyar Yara na ɗaya daga cikin wuraren da ake samun cinkoso, baya ga kuma rashin lafiya da ake fama ita a yanzu.

A karshe hukumar tace zuwan gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sauke likitoci sama da 250, kuma ƙofar su a buze take ga duk mai Korafi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kotu ta bada umarni ga jami’an tsaro da hukumar Hisbah kan su dakatar da kama Mansura Isah

Published

on

Babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai Shari’a Abdullahi Liman, ta takadar da hukumar Hisba da kwamishinan ƴan sanda da kuma mataimakin babban Sifeton ƴan sandan kasar nan daga kama Mansura Isa.

Mai Shari’a Liman ya ayyana cewar ya yi hani ga waɗanda akayi karar ko ƴan korensu ko wakilansu, ko kuma wasu masu aiki amadadinsu daga kamawa ko tsorataswa ko gayyata har zuwa lokacin da za’a saurari kowane ɓangaren.

Wannan umarni dai ya samu ne a cikin wata ƙara mai lamba 159/2024, wadda Mansura Isah ta shigar tana karar hukumar Hisba da kwamishinan ƴan sandan jihar Kano.

Kotun ta sanya ranar 15 ga wannan watan dan sauraron kowane bangare a shari’ar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Zamu farfaɗo da masana’antun ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano – Kwamishina

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta farfaɗo da masana’antun yin saƙa na ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar nan, domin samawa matasa aiki ta yadda za su dogara da kansu.

Kwamishinan ciniki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ne ya bayyana hakan, yayin da ya ziyarci masana’antar saƙar kayayyaki ta ƙaramar hukumar Kura yau Laraba, domin duba halin da take ciki tare da duba yadda za’a farfaɗo da ita daga dogon suman da ta yi.

Tun dai a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, a shekarar 2014, ne ya samar da injina a masana’antar, amma tsohuwar gwamnatin Kano da ta ganata ta yi watsi da masana’anatar.

Yayin duba masana’antar Kwamishinan cikinki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya kuma bada tabbacin farfaɗo da masana’antar yin saƙar ta ƙaramar hukumar Kura da ma na faɗin jihar nan, domin samawa matasa ayyukan yi.

Da yake yiwa Dala FM Kano, ƙarin bayani babban sakataren ma’aikatar ciniki da masana’antu na jihar Kano, Muhammad Yusuf Ɗan-duwa, ya ce, farfaɗo da masana’antar ta Kura, na zuwa ne bisa ƙokarin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan ma’aikatar Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, domin samawa matasa ayyukan yi.

Ya kuma ce yadda tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta wofantar da masana’antar tsawon lokaci, a yanzu gwamnatin su za ta yi duk mai yiyuwa, domin ganin an ta ci gaba da aiki ka’in da na’in.

Tun dai a shekarar 2014 ne aka samar da injina a masana’antar, amma tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta wofantar da aikin, lamarin da ya sa aikin ya tsaya cak, inda gwamnatin Kano mai ci a yanzu ta ce za ta farfaɗo da ita domin samawa matasa aikin yi, da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.

Continue Reading

Trending