Wasanni
Major Sunday Cup: Magoya baya su yi hakur – Kyaftin din Railway Jogana
Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Railway Jogana, Alkasim Idris Garba Jogana ya ja hankalin sauran kungiyoyin da suka rage a gasar cin kofin Major Sunday da ake gudanarwa a Jogana dake karamar hukumar Gezawa da su kara yin hakuri wajen ganin an gudanar da gasar lafiya.
Alkasim Idris ya tabbatar da hakan ne a lokacin da kungiyar su ta samu nasarar kai bantan ta a gasar zuwa wasan kusa da na karshe a hannun Dan Ladi United da ci biyu da nema.
Ya ce”Dole ne sai magoya bayan kungiyoyin da ma kungiyoyin sun yi hakuri, su karbi sakamakon wasan duk yadda ya samu ba sai an tayar da rikici ba, duk wanda ya zo wannan matsayin ya sani cewa sa a ce”.
Shi kuwa Kyaftin din Dan Ladi United, Idris Umar ya ce”Nasara rabo ce ba iyawar mutum ba ce, kuma ina yi musu fatan nasara”.
Shi kuwa Ahmad Coach Dan Madanho shi ne shugaban kwamitin shirya gasar ya ce”kamata a rinka daukar kaddara a wasa, kuma harkar kwallon kafa dole sai da hakuri”.
Norway Academy da Jogana United da FC Tsamiyar Kara da FC Railway Jogana ne suka rage a gasar wanda za su fafata a wasan kusa da na karshe.
Wasanni
Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.
Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.
Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.
Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.
Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.
Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.
Wasanni
Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba
Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.
Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.
Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.
Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.
Wasanni
Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.
Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.
Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.
A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.
Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su