Connect with us

Wasanni

Kwankwasiyya United ta mika ta’aziya ga Kano Pillars da Rarara Kahutu

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Samba Kurna FC wadda a yanzu ta koma Kwankwasiyya United, ta mika sakon ta’aziyar ta ga iyalan shugaban kungiyar masu horaswa na jihar Kano, Danlami Akawu.

Cikin wata sanarwa da mai horas da kungiyar, Mukhtar Abdullahi Shu’aibu wato Coach Teacher ya sanyawa hannu, ta cikin shafina masu horaswa na tashar Dala FM a watsapp.

Sanarwar ta ce a madadin shugabannin masu horarwa da magoya baya na Kungiyar, karkashin Jagorancin, Alh Ali Nayara, ta mika ta’aziyyar ta ga iyalan kungiyar masu horarwa ta kasa reshen jihar Kano, kungiyoyin kwallon Kafa ta Kano Pillars da Rarara Kahutu bisa rasuwar mai horaswa Danladi Usman (Akawu) kuma jami’in a Kano Pillars da Sakatare na Rarara Kahutu Wanda su ka ranar Asabar 13 ga watan Fabrairu, 2021 bayan gajeriyar jinya.

 

Wasanni

Wasan sada zumunta: Wudil KUST ta fafata da Wudil National Star

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta jami’ar Wudil wato Wudil KUST ta yi canjaras da Wudil National Star.

Yayin da FC Samba Wudil ta doke Wudil Super Eagles da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

One to tell 10: Mu na godiya bisa zuwa Tofa Premier da mu ka yi – Coach Auwalu

Published

on

Masu horas da kungiyar kwallon kafa ta One to tell 10, Auwalu Dan Atete da Malan Bello, sun yabawa sauran takwarorin su masu horaswa da kuma hukumar kwallon kafa ta jihar Kano, bisa nasarar da kungiyar ta samu na shiga gasar Tofa Premier.

Masu horaswar sun yabawa shugabancin hukumar kwallon kafa ta jhar Kano karkashin Dr Sharu Rabi’u Inuwa Ahlan bisa jajircewa da ya yin a ganin an inganta harkar wasanni a jihar Kano.

Shi kuwa shugaban kungiyar kwallon kafa ta Man Blues Rumfa, Nasiru Usman Na Malam, ya taya kungiyar kwallon kafa ta Man Blues Rumfa, murnar shiga gasar cin kofin Tofa Premier na jihar Kano.

Cikin wata sanarwa da Nasiru Usman Na Malam ya aikewa sashin wasanni na Dala FM a shafin watsapp na masu horaswa.

Continue Reading

Wasanni

Wasan sada zumunta: Dabai Warriors ta yi kunnen doki da Golden Bullet

Published

on

Sakamakon wasannin sada zumunta da a ka fafata a Kano.

Dorayi Babba Lions -0 Ayaga Action-1

Dabai Warriors-1 Golden Bullet- 1

FC Yalwa-0 Kano Municipal-0

Dawaki academy

Wasannin da za a fafata

FC Kano Lions Amo Boys da Rimin Gata

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!