Connect with us

Labarai

AN YI BARKEWAR CUTAR KWALARA A KARAMAR HUKUMAR GWARZO

Published

on

Rahotanni daga karamar hukumar Gwarzo a nan Kano na nuni da cewar mutane takwas ne suka rasa rayukan su a yayin da sama da mutane arba’in ke kwance a gidajen su wasu kuma a Asibitin garin sakamakon kamuwa da cutar amai da gudawa.
Kauyukan da annobar ta shafa sun hada da Lakwaya, Kofar Arewa, Kofar Yamma, Abuja Kwatas, Gwarzo Bare-bari da kuma Unguwar.
A cewar daya daga cikin Matasan Karamar Hukumar mai suna Ibrahim Sale ya yi karin bayani game da halin da suka tsinci kan su tun daga lokacin da cutar ta bulla a yankin.
A ziyarar da tawagar gidan Rediyo Dala ya kai Kauyukan da wannan cutar ta Kwalara ta bulla, ya gano yadda da yawa daga cikin wadanda lamarin ya shafa ke cikin wani mawuyacin hali harma kuma suke bayyana yadda cutar ta faru dasu.
Sai dai ko da muka isa Babban Asibitin dake karamar Hukumar ta Gwarzo mun iske yadda mutane ke tururuwa domin kawo ‘yan uwan su da suka kamu da cutar ta Amai da Gudawa ga kuma abun da wasun su ke cewa.
Koda muka tuntubi shugaban karamar Hukumar ta Gwarzo Injiya Bashir Kutama ta wayar tarho wanda yake kan hanyar sa ta zuwa Abuja ya tabbatar da Bullar Cutar a karamar Hukumar tasa harma ya kara da cewa tuni suka siyi magungunan cutar domin baiwa mutanen da lamarin ya shafa kyauta.
Amma wasu daga cikin ‘yan uwan marasa lafiyar sun tabbatar mana da cewa ko kadan ba’aba su maganin cutar kyauta ba kuma duk wanda yakai mara lafiyar sa aka rubuta masa magani sai dai ya siya da kudin sa.
A nasa bangaren Hakimin karamar Hukumar ta Gwarzo Alhaji Shehu Kabiru Bayero yace a baya an sanar dashi bullur cutar kafin tayi kamari domin ba kasafai mutane ke sanar da su ba.
Munyi kokarin jin ta bakin ma’aikatar lafiya ta jihar kano amma kokarin namu bai kai ga gaci ba.
Al’ummar ta Karamar Hukumar ta Gwarzo sun yi kira ga Mahukunta da su kawo musu dauki duba da irin kamarin da cutar ta yi a wadannan Kauyuka.

Labarai

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.

Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.

Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.

Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala

Published

on

Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.

“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.

Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.

Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.

Continue Reading

Labarai

Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge

Published

on

Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.

Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.

Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.

A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.

Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.

Continue Reading

Trending