Connect with us

Wasanni

Jet Bombers: An dakatar da dan wasa Shamsu Musa da jami’in kungiyar

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta jihar Kano ta dakatar da guda daga cikin mahukuncin kungiyar kwallon kafa Jet Bombers, Haruna Mai Nama daga shiga cikin harkoin kwallon kafa har na tsawon shekara guda.

Cikin wata takardar hukumar wasanni da ta fitar mai dauke da sa hannun babban sakataren hukumar, Shehu Buhari ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce bisa kunshin rahoton da ta karba a wasan da kungiyar ta fafata dabDawaki Ajax a gasar ajin matasa rukuni na daya a ranar 12-02-2021 a filin Mahaha cewa, Haruna Mai Nama ya ci zarafin mataimakin sakataren hukumar kuma wanda shi nensakataren shirya gasar tare da gaya masa kalamu marasa dadi. Sannan kuma sun saka dan wasan Dorayi Warriors wanda yake buga gasar Tofa Premier ya kuma dawo ya na buga gasar ajin matasa rukuni na daya na Ahlan Cup.

Yanzu haka hukumar ta yanke shawararkwacewa kungiyar Jet Bombers maki uku tare da kwallaye uku a wasan, sannan kuma dan wasan Shamsu Musa an dakatar da shi daga halartar wasanni da hukumar kwallon kafa ta jihar Kano ta ke shiryawa.

 

Wasanni

Wasan sada zumunta: Wudil KUST ta fafata da Wudil National Star

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta jami’ar Wudil wato Wudil KUST ta yi canjaras da Wudil National Star.

Yayin da FC Samba Wudil ta doke Wudil Super Eagles da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

One to tell 10: Mu na godiya bisa zuwa Tofa Premier da mu ka yi – Coach Auwalu

Published

on

Masu horas da kungiyar kwallon kafa ta One to tell 10, Auwalu Dan Atete da Malan Bello, sun yabawa sauran takwarorin su masu horaswa da kuma hukumar kwallon kafa ta jihar Kano, bisa nasarar da kungiyar ta samu na shiga gasar Tofa Premier.

Masu horaswar sun yabawa shugabancin hukumar kwallon kafa ta jhar Kano karkashin Dr Sharu Rabi’u Inuwa Ahlan bisa jajircewa da ya yin a ganin an inganta harkar wasanni a jihar Kano.

Shi kuwa shugaban kungiyar kwallon kafa ta Man Blues Rumfa, Nasiru Usman Na Malam, ya taya kungiyar kwallon kafa ta Man Blues Rumfa, murnar shiga gasar cin kofin Tofa Premier na jihar Kano.

Cikin wata sanarwa da Nasiru Usman Na Malam ya aikewa sashin wasanni na Dala FM a shafin watsapp na masu horaswa.

Continue Reading

Wasanni

Wasan sada zumunta: Dabai Warriors ta yi kunnen doki da Golden Bullet

Published

on

Sakamakon wasannin sada zumunta da a ka fafata a Kano.

Dorayi Babba Lions -0 Ayaga Action-1

Dabai Warriors-1 Golden Bullet- 1

FC Yalwa-0 Kano Municipal-0

Dawaki academy

Wasannin da za a fafata

FC Kano Lions Amo Boys da Rimin Gata

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!