Connect with us

Wasanni

An fafata a wasan Dambe tsakanin Arewa da Kudu

Published

on

‘Yan wasan damben gargajiya daga bangaren Arewa da Kudu, Gurumada ne ke fafata wa a filin wasan damben gargajiya na Ado Bayero square dake unguwar Sabon Gari a jihar Kano.

Daga cikin ‘yan wasan damben akwai Ali kanin Bello da bahagon-shagon sojoji da dogon Zee Y da shagon Bahagon Audu Argungu dukkaninsu sun fito ne daga bangaren yankin Arewa.

Abangaren yankin kudu akwai Abdul razak Ebola, da dan Alin bata Isarka da Bahagon dage da Bahagon Madaki da dasauran su.

Su kuwa bangaren yankin Gurumada sun hadrda Dogon manu kwalabe da shagon Bahagon dan Mutuwa da Shagon mai Takwasara da dai sauransu.

A damben da aka gwabza tsakanin Shagon Bahagon Sani mai Maciji da Bahagon Shagon Sojoji turmi uku a ka yi babu wanda ya doke abokin damben shi.

Autan Ali kanin Bello da Shagon Bahagon dan mutuwa suma turmi uku suka kwashe suna dauki ba dadi babu wanda ya samu nasara a tsakaninsu.

Shagon Dogon Autan dan Bunza da Autan Sama’ila turmi daya aka rabasu sakamakon Autan sama’ila yaji ciwo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Unity Cup: M.Y Jamil za ta barje gumi da Zoo United

Published

on

A ci gaba da gasar Unity Cup ajin matasa da ake fafatawa a jihar Kano, a yammacin ranar Juma’a ne kungiyar kwallon kafa ta M.Y Jamil za ta kara da Zoo United a filin wasa na Mahaha Sport Complex dake Kofar Na’isa a cikin filin Kano United.

Soccer Strikes za ta kece raini da Clever Warriors a filin wasa na Sky Limit dake Mahaha.

Kano Rovers za ta fafata da Gama Emirates a filin wasa na Gwagwarwa Mini Stadium.

Dabo Babies za ta buga da Dabo Babies a filin wasa na Diso United dake Mahaha.

Wasannin duka za a fafata su ne da karfe hudu na yammacin ranar Juma’a.

Continue Reading

Wasanni

Kano: Sakamakon gasar Unity Cup

Published

on

Sakamakon wasannin kwallon kafar da aka fafata a yammacin ranar Alhamis a jihar Kano.

Admiral United 0-2 Ramcy FC

Leeders FC 2-0 Royal Form

Kano United 5-2 Zango Academy

Continue Reading

Wasanni

Kwallon Golf: Na fara zuwa filin wasan Golf tun 1977 – Malam Isah Lafiya

Published

on

Wani dan wasan kwallon Golf, Malam Isah Lafiya, ya ce ya fara wasan kwallon Golf sakamakon ya kasance mai matsayin daukar jakar ‘yan wasa.

Malam Isa Lafiya ya kuma ce tun ya na daukar jakar ‘yan wasan kwallon Golf ta na rinjayar shi, har ta kai gay a kai matsayin fara buga wasan.

Wakilin mu Musa Abdu daga filin wasan kwallon Golf na jihar Kaduna ya turo mana da rahoto.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!