Connect with us

Wasanni

Dambe: Shagon Sama’ila daga Kudu ya kashe Bahagon Shagon Sanin Kurna daga Arewa

Published

on

Daga filin wasan Dambe na Ado Bayero Square dake jihar Kano, an fafata a ranar Juma’a 20 ga watan Fabrairu 2021, ‘yan Damben Arewa sun fito sun nemi abokan karawa daga Gurumada da Kudawa sai dai hakan bai samu ba daga karshe mawaka ne su ka yi zaben abokan karawa.

Ajin manya na ‘yan Damben Shagon Sama’ila na Kudu ya kashe Bahagon Shagon Sanin kurna na Arewa.

Adamu Bahagon Dage da Shagon Reza ba kisa.

Bahagon Danja wutar baya ya buge Dogon Zee Y a turmin farko.

Shagon Bahagon Garkuwar Musa ya doke Dogon Manu Kwalabe a turmin farko.

Sama’ila Shagon Alabo ya kashe Dogo na Karkarna a turmin farko.

Shagon Fatalwa da Shagon Reza babu kisa.

Shagon Bahagon Danja ya sake kashe Dogo na Karkarna a karo na biyu.

Shagon-Shagon Buhari da Shagon Reza Bunza har turmi biyu ba kisa, yau sau uku Shagon Reza yana fafatawa saidai babu nasarar kisa.

Mola-Mola da Shagon Bahagon Danja ba kisa yau wasanni uku Shagon Bahagon Danja ya kara ya samu nasara a Dambe  biyu saidai a wasan karshe ne nasarar ba ta zo ba kamar yadda wakiliyar mu Hadiza Ado Jinta daga gidan Dambe ta turo mana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Unity Cup: M.Y Jamil za ta barje gumi da Zoo United

Published

on

A ci gaba da gasar Unity Cup ajin matasa da ake fafatawa a jihar Kano, a yammacin ranar Juma’a ne kungiyar kwallon kafa ta M.Y Jamil za ta kara da Zoo United a filin wasa na Mahaha Sport Complex dake Kofar Na’isa a cikin filin Kano United.

Soccer Strikes za ta kece raini da Clever Warriors a filin wasa na Sky Limit dake Mahaha.

Kano Rovers za ta fafata da Gama Emirates a filin wasa na Gwagwarwa Mini Stadium.

Dabo Babies za ta buga da Dabo Babies a filin wasa na Diso United dake Mahaha.

Wasannin duka za a fafata su ne da karfe hudu na yammacin ranar Juma’a.

Continue Reading

Wasanni

Kano: Sakamakon gasar Unity Cup

Published

on

Sakamakon wasannin kwallon kafar da aka fafata a yammacin ranar Alhamis a jihar Kano.

Admiral United 0-2 Ramcy FC

Leeders FC 2-0 Royal Form

Kano United 5-2 Zango Academy

Continue Reading

Wasanni

Kwallon Golf: Na fara zuwa filin wasan Golf tun 1977 – Malam Isah Lafiya

Published

on

Wani dan wasan kwallon Golf, Malam Isah Lafiya, ya ce ya fara wasan kwallon Golf sakamakon ya kasance mai matsayin daukar jakar ‘yan wasa.

Malam Isa Lafiya ya kuma ce tun ya na daukar jakar ‘yan wasan kwallon Golf ta na rinjayar shi, har ta kai gay a kai matsayin fara buga wasan.

Wakilin mu Musa Abdu daga filin wasan kwallon Golf na jihar Kaduna ya turo mana da rahoto.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!