Labarai
Gwamnati ta yi kokarin kawo masalaha da ‘yan Adaidaita – Fasinjoji

Wasu daga cikib fasinjoji a jihar Kano, sun ce kamata ya yi gwamnati ta yi kokarin kawo masalaha tsakanin su da masu Babur din Adaidaita Sahu, bisa muhimmancin da suke da shi a wurin al’umma.
Wannan batun na zuwa ne adaidai loakcin da masu baburan Adaidaitan suka tsunduma yajin aikin gama gari a ranar Litinin.
Hakan ya sanya wasu fasinjoji sun koka dangane da rashin abin hawa da suka fuskan ta a ranar ta Litinin.
Fasinjojin da suka ce tun karfe bakwai na safe suke jiran baburan adaidaita sahu, domin tafiya wuraren da za su je, amma ba su samu abun hawa ba.
A cewar su”Kamata ya yi gwamnati ta yi kokarin kawo masalaha ga direbobin duba da muhimmancin su ga alumma”.
Wasu daga cikin matuka baburan sun ce sun shiga yajin aikin ne, saboda nuna rashin jin dadin su a kan dokar biyan Naira 100 da gwamnatin Kano ta bullo musu da shi.
Wakilin mu Ahmad Rabiu Ja’en, ya rawaito cewa wasu daga cikin fasinjojin na hawa motocin Kurkura, yayin da wasu kuwa ke takawa da kafa, domin zuwa inda za su je.
Labarai
Kotu ta dakatar da yin muƙabala da Malam Abduljabbar

Kotun majistrate mai lamba 12, dake zaman ta gidan Murtala karkashin mai shari’ah Muhammad Jibrin ta dakatar da gwamnatin Kano daga gabatar da tattaunawa tsakanin malam Abduljabbar da malam Kano a ranar Lahdi mai zuwa.
Hakan dai ya biyo bayan shigar da ƙarar da wani lauya mai zaman kan sa, Ma’aruf Yakasai ya yi.
Labarai
Da za mu ji tsoron Allah zai azurta mu ta inda bama zato – Alhuzaifiy

Limamin Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama dake birnin Madina Sheikh Aliyu Bn Abdurrahman Alhuzaifiy ya yi kira ga al’ummar Musulmi da suji tsoron Allah Madaukakin sarki.
Alhuzaifiy ya yi kiran ne a huɗubar Juma’a da ya gabatar a masallacin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama.
Ya ce, “Da mutane za suji tsoron Allah da Allah ya azurta su ta inda basa zato”.
Ya kuma ce, “Jin tsoron Allah ya na kawo wa al’umma alkhairi mai tarin yawa, yana kuma dauke musu talauci da tsoro a cikin su”.
Ya ƙara da cewa, “Mafi girman ni’imar da Allah zai yiwa mutum ita ce ni’imar imani, da ta Alqur’ani, da zaman lafiya, da ni’imar Lafiya ta jiki”. A cewar Sheikh Alhuzaify.
Wakilin mu Umar Yakubu Ilu ya rawaito mana cewa Sheikh Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy ya kuma ce, hanyar samun cikakken tsaro ita ce bin tafarkin Allah da dokokin da Allah yasa a cikin Alqur’ani, amma dokokin da bana Allah ba basa kawo cikakken tsaro ga al’umma.
Labarai
Rahoto: A sama mana mafita saboda mu ci gaba da sana’ar mu – Masu figar kaji

Masu sana’ar yanka kaji da figeta a kasuwar Sabon gari dake jihar Kano sun yi korafi kan yadda suka wayi gari da ganin an rushe musu wurin da suke gudanar da sana’ar su a ranar Talata.
A cewar su an rushe musu wajen sana’ar wanda a kalla kulum a na yanka kaji sama da miliyan guda a cikin kasuwar ta su.
Ga cikakken rahoton da wakilin mu Aliyu Wali ya halarci ‘yan Kaji na kasuwar Sabon Gari ga kuma rahoton da ya turo mana.
-
Manyan Labarai1 year ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi1 year ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai12 months ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi1 year ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai5 months ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi1 year ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai1 year ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari
-
Manyan Labarai1 year ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
You must be logged in to post a comment Login
You must log in to post a comment.