Connect with us

Labarai

Rahoto: Kasuwar ‘Yan Kurkura ta bude a Kano

Published

on

Direbobin motar kurkura sun koma daukar fasinjoji da motar maimakon daukar kaya sakamakon tsunduma yajin aiki da direbobin Adaidaita sahu suka gudanar a ranar Litinin.

Wani direban Kurkurar mai suna Yawale Abdu ya bayyana wakilin mu Ibrahim Abdulllahi Soron Dinki cewar, suna daukar mutane domin taimaka masu zuwa wajen harkokin su cikin rangwamen kudi.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Kotu ta dakatar da yin muƙabala da Malam Abduljabbar

Published

on

Kotun majistrate mai lamba 12, dake zaman ta gidan Murtala karkashin mai shari’ah Muhammad Jibrin ta dakatar da gwamnatin Kano daga gabatar da tattaunawa tsakanin malam Abduljabbar da malam Kano a ranar Lahdi mai zuwa.

Hakan dai ya biyo bayan shigar da ƙarar da wani lauya mai zaman kan sa, Ma’aruf Yakasai ya yi.

Continue Reading

Labarai

Da za mu ji tsoron Allah zai azurta mu ta inda bama zato – Alhuzaifiy

Published

on

Limamin Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama dake birnin Madina Sheikh Aliyu Bn Abdurrahman Alhuzaifiy ya yi kira ga al’ummar Musulmi da suji tsoron Allah Madaukakin sarki.

Alhuzaifiy ya yi kiran ne a huɗubar Juma’a da ya gabatar a masallacin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama.

Ya ce, “Da mutane za suji tsoron Allah da Allah ya azurta su ta inda basa zato”.

Ya kuma ce, “Jin tsoron Allah ya na kawo wa al’umma alkhairi mai tarin yawa, yana kuma dauke musu talauci da tsoro a cikin su”.

Ya ƙara da cewa, “Mafi girman ni’imar da Allah zai yiwa mutum ita ce ni’imar imani, da ta Alqur’ani, da zaman lafiya, da ni’imar Lafiya ta jiki”. A cewar Sheikh Alhuzaify.

Wakilin mu Umar Yakubu Ilu ya rawaito mana cewa Sheikh Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy ya kuma ce, hanyar samun cikakken tsaro ita ce bin tafarkin Allah da dokokin da Allah yasa a cikin Alqur’ani, amma dokokin da bana Allah ba basa kawo cikakken tsaro ga al’umma.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: A sama mana mafita saboda mu ci gaba da sana’ar mu – Masu figar kaji

Published

on

Masu sana’ar yanka kaji da figeta a kasuwar Sabon gari dake jihar Kano sun yi korafi kan yadda suka wayi gari da ganin an rushe musu wurin da suke gudanar da sana’ar su a ranar Talata.
A cewar su an rushe musu wajen sana’ar wanda a kalla kulum a na yanka kaji sama da miliyan guda a cikin kasuwar ta su.

Ga cikakken rahoton da wakilin mu Aliyu Wali ya halarci ‘yan Kaji na kasuwar Sabon Gari ga kuma rahoton da ya turo mana.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!