Connect with us

Wasanni

An dage wasanni a Kano saboda yajin aikin ‘yan Adaidaita – Hukumar wasa

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta jihar Kano, ta dage gasar ajin matasa na mataki na daya wato Ahlan League One, sakamakon yajin aikin da masu Baburan Adaidaita Sahu su ka shiga a jihar baki daya.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun, shugaba mai kula da gasar, Ismaeel Idris (Coach Sammer) ya sanya hannu ta cikin shafin masu horaswa na Dala FM Coach’s Forum na watsappa.

Sanarwar ta ce an dage wasanni da za a gudanar a ranar Litinin, makon yajin aikin da ‘yan kungiyar Babura masu kafa uku suke gudanar, saboda saukakawa kungiyoyi zuwa filin wasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Unity Cup: M.Y Jamil za ta barje gumi da Zoo United

Published

on

A ci gaba da gasar Unity Cup ajin matasa da ake fafatawa a jihar Kano, a yammacin ranar Juma’a ne kungiyar kwallon kafa ta M.Y Jamil za ta kara da Zoo United a filin wasa na Mahaha Sport Complex dake Kofar Na’isa a cikin filin Kano United.

Soccer Strikes za ta kece raini da Clever Warriors a filin wasa na Sky Limit dake Mahaha.

Kano Rovers za ta fafata da Gama Emirates a filin wasa na Gwagwarwa Mini Stadium.

Dabo Babies za ta buga da Dabo Babies a filin wasa na Diso United dake Mahaha.

Wasannin duka za a fafata su ne da karfe hudu na yammacin ranar Juma’a.

Continue Reading

Wasanni

Kano: Sakamakon gasar Unity Cup

Published

on

Sakamakon wasannin kwallon kafar da aka fafata a yammacin ranar Alhamis a jihar Kano.

Admiral United 0-2 Ramcy FC

Leeders FC 2-0 Royal Form

Kano United 5-2 Zango Academy

Continue Reading

Wasanni

Kwallon Golf: Na fara zuwa filin wasan Golf tun 1977 – Malam Isah Lafiya

Published

on

Wani dan wasan kwallon Golf, Malam Isah Lafiya, ya ce ya fara wasan kwallon Golf sakamakon ya kasance mai matsayin daukar jakar ‘yan wasa.

Malam Isa Lafiya ya kuma ce tun ya na daukar jakar ‘yan wasan kwallon Golf ta na rinjayar shi, har ta kai gay a kai matsayin fara buga wasan.

Wakilin mu Musa Abdu daga filin wasan kwallon Golf na jihar Kaduna ya turo mana da rahoto.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!