Connect with us

Wasanni

Continue Mandawari: Mun baiwa ‘yan wasan mu na nesa hutu – Sani Baban Iya

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Continue Mandawari ta dakatar da ‘yan wasan ta da suke zuwa daukar horo daga nesa, sakamakon yajin aikin da masu baburan Adaidaita Sahu suka tsunduma a ranar Litinin.

Cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban kungiyar, Sani Baban Iya Mandawari ya sanyawa hannu a kai, kungiyar ta ce duk dan wasan da yake zuwa daga nesa ya yi hakuri ya zauna, har sai an warware matsalar.

Sannan kuma ‘yan wasan da suke kusa za su ci gaba da daukar horo a ranar Talata a filin ta na Mahaha dake Sports Complex.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Unity Cup: M.Y Jamil za ta barje gumi da Zoo United

Published

on

A ci gaba da gasar Unity Cup ajin matasa da ake fafatawa a jihar Kano, a yammacin ranar Juma’a ne kungiyar kwallon kafa ta M.Y Jamil za ta kara da Zoo United a filin wasa na Mahaha Sport Complex dake Kofar Na’isa a cikin filin Kano United.

Soccer Strikes za ta kece raini da Clever Warriors a filin wasa na Sky Limit dake Mahaha.

Kano Rovers za ta fafata da Gama Emirates a filin wasa na Gwagwarwa Mini Stadium.

Dabo Babies za ta buga da Dabo Babies a filin wasa na Diso United dake Mahaha.

Wasannin duka za a fafata su ne da karfe hudu na yammacin ranar Juma’a.

Continue Reading

Wasanni

Kano: Sakamakon gasar Unity Cup

Published

on

Sakamakon wasannin kwallon kafar da aka fafata a yammacin ranar Alhamis a jihar Kano.

Admiral United 0-2 Ramcy FC

Leeders FC 2-0 Royal Form

Kano United 5-2 Zango Academy

Continue Reading

Wasanni

Kwallon Golf: Na fara zuwa filin wasan Golf tun 1977 – Malam Isah Lafiya

Published

on

Wani dan wasan kwallon Golf, Malam Isah Lafiya, ya ce ya fara wasan kwallon Golf sakamakon ya kasance mai matsayin daukar jakar ‘yan wasa.

Malam Isa Lafiya ya kuma ce tun ya na daukar jakar ‘yan wasan kwallon Golf ta na rinjayar shi, har ta kai gay a kai matsayin fara buga wasan.

Wakilin mu Musa Abdu daga filin wasan kwallon Golf na jihar Kaduna ya turo mana da rahoto.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!