Connect with us

Manyan Labarai

Rubutu da karatun tarihi ne ke daƙile ɓacewar sa – Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci al’ummar jihar da su himmatu wajan rubutu da karatun tarihi, domin gudun ɓacewar sa a cikin al’umma.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne, ta bakin kwamishinan harkokin kasuwancin jihar Barista Ibrahim Muktar a wajan kaddamar da wasu litattafan tarihi biyu da malam Ibrahim Aminu Ɗan iya ya rubuta.

Ya ce, “Tarihi abu ne mai muhimmancin gaskiya a cikin al’umma, saboda haka bai kamata a bari ya na shuɗewa ba”.

Anasa jawabin, shugaban taron tsohon minista Ambasada Aminu Bashir Wali ya ce, littattafan za su amfanar da al’umma matuka da gaske.

Shi kuwa marubucin littattafan masanin tarihi malam Ibrahim Aminu Ɗan iya, cewa ya yi an samar da littattafan ne dan mutane su amfana da abubuwan da na baya suka yi.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa littattafan biyu da aka kaddamar sun hadar da darussan farko a tarihin Kano, sai kuma na turanci, The Dabo of Kano.

Labarai

Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.

Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.

Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.

Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.

Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.

Continue Reading

Labarai

Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.

Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.

Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.

Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!