Connect with us

Labarai

Kwararru a fannin lafiya na binciken yadda wata sabuwar cuta mai saurin lahani ta bulla a Kano

Published

on

Kwararru a fannin lafiya, na binciken musababbin bullar wata sabuwar cuta, mai saurin lahani da ake zargin ta samo asali ne daga ruwan sha.

Wannan cuta dai ta bulla ne a Unguwar Warure da ke yankin karamar Hukumar Gwale, a jihar Kano.

Ana zargin dai mazauna Unguwar sun harbu da wata cuta da ba a kai ga gano ta ba, bayan da suka yi amfani da ruwan wata rijiya da ke makabartar Dan-Dolo.

Abin da rahotanni ke zargi shine, amfani da ruwan rijiyar da maƙabartar Ɗandolo ya jikkata mutane 17 a unguwar Warure, inda suka kamu da wata cuta da ta ɓulla wadda ba a santa ba.

Waɗanda suka kamu da cutar sun shaida wa Dala FM, yadda suka riƙa fama da aman majina da zazzaɓi da ciwon kai, sai kuma fitsarin jini.

Wata mata mai suna Siyama, da ta kamu da cutar, ta ce har yanzu akwai wadanda suke cikin tsananin jin jiki sakamakon cutar da suka harbu da ita a gidansu.

“Ni dai jikina da dan sauki-sauki zan ce, domin fitsarin jinin da na ke yi yanzu babu sosai, sai wadanda suka kamu da cutar a gidanmu har yanzu suna jin jiki” a cewar ta.

Yanzu haka dai tuni aka garzaya da mutane 17 zuwa asibitin lura da mafitsara na Abubakar Imam.

Sai dai, Dakta Atiku Ado Muhammad, wanda shine shugaban asibitin na Abubakar Imam, ya ce sun lura cewa cutar tana iya zama annobar kwarai, don haka ne ma su ka yi gaggawar tura su Asibitin koyarwa na Aminu Kano.

“Bisa binciken da muka gudanar, ya nuna  cewa wadannan mutane suna bukatar agajin gaggawa, don haka tuni muka yanke shawarar tura su asibitin koyarwa na Aminu Kano” in ji shi.

Munyi kokarin jin ta bakin ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, sai dai kwamishinan lafiya Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce zai yi karin bayani nan gaba, da zarar sun kammala bincike a kai.

Saurari karin bayanin Dakta Atiku Ado Muhammad game da wannan cuta.

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Labarai

Mata ku ƙara kula da tsaftar jikin ku a gidan auren ku – DCG Dr. Khadijah Sagir Sulaiman

Published

on

Mataimakiyar babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano a ɓangaren Mata, DCG Dakta Khadijah Sagir Sulaiman, ta shawarci matan aure da su ƙara kulawa da tsaftar jikin su musamman kan abinda ya shafi bakunansu, da kuma gaɓoɓin da suke riƙe Gumi a wannan yanayi na zafi da ake ciki.

Dakta Khadijah Sagir, ta bayyana hakan ne yayin rangadin bibiyar auren gatan da gwamnatin jihar Kano ƙarkashin Injiniya Abba Kabir Yusuf, tayi a baya, wanda ta fara da ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a jiya Lahadi, ina zaman ya gudana a ofishin Hisbah na ƙaramar hukumar.

DCG Khadijah, ta kuma ce matuƙar matan auren za su ƙara kulawa da tsaftar jikin nasu, hakan ka iya taimaka musu wajen ƙara wanzuwar zaman lafiya a tsakanin su da mazajen su.

Da take nata jawabin mataimakiyar kwamandan Hisbah ta ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a ɓangaren mata Malama Saratu Sheikh Nasiru Kabara, cewa ta yi, ziyarar rangadin abu ne da tayi farin ciki, kasancewar bata taɓa samun makamanciyar ziyarar ba sama da shekaru 15 da fara aikin ta a can.

Wakiliyarmu Hadiza Balanti Ceɗiyar ƴan Gurasa ta rawaito cewa, yayin ziyarar rangadin bibiyar auren gatan Dakta Khadijah Sagir Sulaiman, ta kuma rarraba wa matan auren kayan goge baki, da kuma abubuwan da ke ɗauke sansanar jiki mara daɗi wato alumun, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Kwamitin bincike kan tsohuwar gwamnatin Ganduje ya fara zama.

Published

on

Kwamitin da gwamnatin jahar kano ta kafa dan binciken gwamnatin Ganduje, ya bayyana irin sigar da masu korafi za su gabatar da ƙorafi a gaban kwamitin.

Gwamnatin jahar kano ta kafa kwamitin karkashin jagorancin mai Shari’a Faruk Lawan, dan bincike akan zargin da gwamnati mai ci take yiwa gwamnatin da ta shude akan yadda akayi tasarrafi da dukiyar jahar Kano.

A yayin zaman kwamitin mai Shari’a Faruk Lawan, ya bayyana cewa duk wani mai korafi zai rubuto korafinsa a takadda, domin gabatar wa a gaban kwamitin.

Gwamnatin dai ta kafa kwamatoci guda 2 dan bincike akan yadda akayi tassarifi da dukiyar jahar kano, da kuma abin da ya janyo ɓatan ƙananan yara, da rikice-rikicen siyasa wadanda akayi zargin sun faru a tsawon shekaru takwas na gwamnatin Ganduje.

Continue Reading

Trending