Connect with us

Labarai

Rigakafin Corona: Za mu fara wayar da kan jama’a tukuna – Ganduje

Published

on

Gwamnatin Kano za ta bullo da shirin wayar da kan jama’a musamman mazauna karkara, kan muhimmancin rigakafin cutar Corona, bayan da gwamnatin ta karbi kason farko na wannan allura a daren ranar Litinin.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce akwai bukatar a wayar da kan jama’a, kafin a fara musu ita, kasancewar wasu na kokarin sanya fargaba a zukatan jama’a game da wannan rigakafin.

“Mun yanke shawarar bullo da shirin wayar da kan jama’a, sakamakon muhimmancin yadda za a shawo kan annobar Covid-19 da ta kasance barazana ga duniya” in ji gwamna Ganduje

Wannan dai na zuwa ne yayin da wasu gwamnonin jihohin kasar nan suka fara karbar allurer rigakafin, bayan da kason farkonta ya shigo Najeriya.

Ngong Cyprian likita ne da ya kasance mutum na farko da aka fara yiwa allurar rigakafin cutar ta Corona, wanda kamfanin AstraZeneca ya samar.

Yayin taron wayar da kan wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce zasu cigaba da Kiran rukunonin al’umma daban daban don dai fadakar da mutane muhimmancin allurar rigakafin domin Kare kamuwa da ita

tun farko a nasa jawabin, shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Kano, Muhammadu Baffa Takai, ya ce zasu taka muhimmiyar rawa wajen ganin aikin allurar rigakafin Corona ya samu nasara anan Kano batare da wata turjiya ba

“Mu ne muke da gudun mowar da za mu bayar, saboda kusancin da muke da shi da jama’a, za mu yi kokari na ganin mun wayar da kan mutane, saboda wannan cutar dole ne a tunkare ta da gaske” In ji shi.

A halin da ake ciki, sama da mutane dubu 1 da 950 annobar Korona ta kashe a Najeriya daga cikin akalla sama da dubu 150 da suka kamu da ita, yayin da kuma dubu 137 suka warke.

An dai gudanar da taron wayar da Kan shugabannin kananan hukumomin ne tare da shugabannin direbobin adaidaita sahu da NATO, da NURTW.

Labarai

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi ya tsallake karatu na ɗaya a majalisar dokokin Kano

Published

on

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke jihar Kano, ya tsallake karatu na ɗaya a zauren majalisar dokokin jihar.

Ƙudurin ya kai wannan mataki ne yayin zaman majalisar na yau Laraba, ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan da akawun majalisar Alhaji Bashir Idris Ɗiso, ya gabatar da karatun na ɗaya.

Har ila yau, yayin zaman na yau, majalisar ta buƙaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta tallafa wa wasu kanikawa da kafintoci bisa iftila’in gobarar da ta ƙone musu kaya na miliyoyin Naira, tare da asarar rayuka a kan titin Lawan Dambazau.

Majalisar ta buƙaci hakan ne biyo bayan ƙudurin gaggawa da wakilin ƙaramar hukumar Birni da kewaye Alhaji Sarki Aliyu Daneji ya gabatar.

Yayin gabatar da ƙuɗurin, ɗan majalisar ya nemi gwamnatin data tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa domin rage musu raɗaɗin iftila’in.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin da ta ɗaga darajar asibitin garin Gano, zuwa matakin babban asibiti domin ƙara inganta kiwon lafiya a yankin har ma da sauran yankuna, kamar yadda ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Shu’aibu Rabi’u ya buƙata.

Wakilinmu na majalisar Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, a dai zaman na yau Laraba, shi ma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙaraye, Injiniya Ahmed Ibrahim, ya gabatar da ƙudurin neman gwamnatin Kano ta gina titi a hanyar da ta tashi daga mahaɗar titin zuwa sansanin horas da matasa ƴan hidimar ƙasa, ta bi ta Kurugu da Dederi har zuwa Yammedi duk a yankin ƙaramar hukumar Ƙaraye.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sauya shugaban hukumar tattara haraji na jihar

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin Dakta Zaid Abubakar, a matsayin sabon shugaban hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta jihar Kano, da kuma Kasim Ibrahim a matsayin babban daraktan hukumar.

Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da aka aikowa Dala FM Kano, a daren jiya Laraba.

Sanarwar ta ce, tsohon shugaban hukumar Alhaji Sani Abdulkadir Dambo, an mayar da shi ne a matsayin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari, wanda kuma sauye-sauyen za su fara aiki nan take.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur: Fadar shugaban ƙasa kiyi wani abu dan mutane su samu sauƙi – Ƙungiyar Nothern Concern Soliderity

Published

on

Yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a ƙasar nan, ƙungiyar da ta damu da abubuwan da suka shafi arewacin ƙasar nan ta Northern Concern Soliderity, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace dan ganin mutane sun samu wani sauƙi.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar, kuma sakataren riƙo na zauren gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Kwamared Saddat Usman Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, lokacin da yake nuna takaici kan irin wahalar da al’ummar ƙasa suke sha wajen shan man Fetur a gidajen man.

Ya ce duba da halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kansu a ciki, akwai buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki su kawo ƙarshen wahalar man Fetur ɗin da aka fama da ita.

Kwamared Saddat Maiyaƙi, ya kuma haƙurƙurtar da al’ummar ƙasar nan kan halin ƙuncin rayuwar da suka samu kai a ciki, inda ya yi fatan komai ya zo karshe cikin ƙanƙanen lokaci.

Continue Reading

Trending