Connect with us

Labarai

Ranto Biliyan 300 a China: Kungiyoyi na karar gwamnatin Kano a kotu

Published

on

Babbar kotun tarayya mai lamba uku da ke zamanta a unguwar Gyadi-gyadi, karkashin mai shari’a Sa’adatu Ibrahim Mark, ta sanya ranar 19 ga watan gobe domin ci gaba da sauraron wata kara da Kwamared Kabiru Sa’idu Dakata da kungiyar CAJA su ka shigar, su na karar gwamnatin Kano dangane da yunkurin ranto kudi sama da Biliyan 300 daga kasar China.

A zaman kotun na ranar Litinin, wasu lauyoyi kimanin 10 karkashin Farfesa Mamman Lawan Yusufari SAN sun bayyana a gaban kotun da takardu su na rokon kotun da ta sanya su a cikin shari’ar domin su kare shugaban majalisar Dattawa.

An kuma yi muhawara tsakanin lauyan masu kara, Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzurci da lauyan wadanda aka yi kara barista M N Duru a kan batun kotun ko ta na da hurumin yin shari’ar ko akasin hakan.

Cikin wadanda a ka yi kara, sun hadar da majalisar dokoki ta jihar Kano da shugaban majalisar Dattawa da babban bankin kasar nan CBN da ma’aikatar kudi da wani banki dake kasar China da kuma ofishin jakadanci na kasar ta China.

Farfesa Mamman Lawan Yusufari SAN, wanda shi ne lauyan shugaban majalisar Dattawa ya ce, sun roki kotun da ta karawa sassan shari’ar lokaci domin yin nazari a kan takardun shari’ar.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya zanta da lauyan masu kara, Bashir Yusuf Wanda ya bayyana cewar, ranto wadannan makudan kudade domin yin aikin jirgin kasa mai aiki da lantarki ba zai haifar wa jihar Kano  da mai ido ba.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending