Labarai
Rahoto: Ba na jin dadin ganin mai nakasa ya na bara – Gurgu

Wani mutum mai lalurar kafa wato Gurgu ya ja hankalin al’umma masu nakasa da su nemi sana’ar dogaro da kai maimakon yin bara akan tituna.
Mutumin mai suna Muhammad Auwal, mazaunin unguwar Janbulo, mai shekaru hamsin a duniya ya bayyanawa wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki cewar, bai taba yawan bara ba, da sana’ar hada takalma ya yi aure, yanzu haka yana da ‘ya’ya biyar.
Ya ce, “Idan na ga mai wata nakasa ya na bara ba na jin dadi, musamman ma idan yafi ni lafiya, kamata ya yi mai nakasa ya samu aikin dogaro da kansa maimakon fita yawon bara”.
Labarai
Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.
Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.
Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.
Labarai
Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.
Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.
Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.
Labarai
Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.
Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.
Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.
Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.
-
Nishadi1 year ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai1 year ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai1 year ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi1 year ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai6 months ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi1 year ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai1 year ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari
-
Manyan Labarai1 year ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
You must be logged in to post a comment Login
You must log in to post a comment.