Connect with us

Labarai

Zargi: Matashin da ya addabi mutanen Goron Dutse ya shiga hannu

Published

on

Daga unguwar Yalwa dake yankin Goron Dutse, layin Ƴan Kaɗi bayan gidan malam Nasidi Abubakar, a karamar hukumar Dala, wani matashi mai suna Saddiqu mai laƙanin (mai idon) , a zargin sa da addabar al’ummar yankin da sace-sace, har ma a makon da ya gabata a ke zargin ya gayyato wasu guggun matasa daga wasu unguwannin suka farwa mutanen yankin da sara da suka har ma da satar wayoyi da kudi.

Abba Abubakar matashi ne mai shekaru ashirin (20) da haihuwa, kuma shi ne wanda a ke zargin an sara a lokacin da ɓata garin su ka shiga unguwar, ya ce “Ban san hawa ba ban san sauka ba, sai ji na yi an hau ni da sara lamarin da ya sa na gudu babu shiri, har kuma na shiga wani gida, amma saboda an sare ni a hannu na kasa rufe gidan da na shiga, saboda haka ina kira ga mahukunta a bi min hakki na”.A cewar matashi Abba.

Haka zalika wasu matasan da a ka bayyana cewa, ɓata garin sun rutsa da su har cikin shagon da su ke kwana, su ma mun zanta da mahaifin su, Alh Danlami Abubakar Goron Dutse, wanda ya ce, “Matasan ɗauke da muggan makamai sun yi kokarin shiga har inda ƴaƴa na su ke kwana, da yaran su ka kula, su ka shiga bandakin cikin dakin, su ka bar wayoyin su da kudi har Naira dubu sittin,  kuma mu na yabawa jami’an tsaro da wannan ƙoƙarin na su”. Inji Danlami.

Idris Abubakar Idris wanda a ka fi sani da Babangida ɗan Malam ya ce, “Mun ji daɗi da ya shiga hannu, saboda ya na addabar mu da yawan sace-sace“.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending