Connect with us

Labarai

Gasar Premier: Magoya bayan shirin sun mika kayan abinci zuwa gidan marayu

Published

on

Dandalin magoya shirin gasar Firimiya ta kasar Ingila a tashar Dala FM dake Kano, sun mika kayayyakin abinci zuwa gidan marayu na Nasarawa.

Magoya bayan shirin wadanda su ke marawa kungiyoyin gasar Firimiya na Ingila, sun mika kayayyakin ne ga shugabar gidan Aishatu Sani Kurawa a karshen makon nan 15-05-2021.

Shugaban shirin Tijjani Adamu kuma mai gabatar da shrin tare da Abba Haruna Idris, su ne suka jagoancin mika kayayyakin abincin wanda su ka hadar da Taliyar ‘yan yara da biskit da kuma lemukan yara, zuwa wajen shugabar gidan.

Cikin mambobin dandalin gasar da su ka samu damar halartar mika kayayyakin akwai: Magoyin bayan kungiyar Arsenal, Sadik Nahaja sai kuma Musa Ali tare da Isah Idris Umar Madobi.

Sauran sun hadar da Umar Yakasai Arsenal, Ashir Ya’u Muhammad, Aminu Matacciya Sheka, Kamisu Bala Tsamawa B. Khamis, Al’amin AA Kurna, Anas Saminu Kura Liverpool, Saminu Zawa’I Mandawari da kuma Usman S Bala.

Hotunan magoya bayan shirin gasar Firimiya tare da masu gabatarwa.

Wannan dai shi ne karo na farko da magoya bayan shirin gasar Firimiya ta kasar Ingila a jihar Kano bangaren tashar Dala FM 88.5 Kano, su ka mika kayayyakin abinci zuwa gidan marayu a jihar Kano.

Kayayyakin abincin da magoya bayan shirin a jihar Kano da kewaye na Najeriya su ka mika kayan abincin ga marayu.

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending