Connect with us

Wasanni

Sharada United: Mun dawo faggen daga – Ya’u Jaja

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Sharada United da ke karamar hukumar birni a jihar Kano, ta dawo ci gaba da daukar horo bayan da ta shafe dogon lokaci ta na hutu.

Mai kungiyar, Ya’u Ahmad Jaja Sharada ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya aikewa sashin wasanni na Dala FM Kano.

Sanarwar ta bayyana cewa yanzu haka Sharada United ta dawo daukar horo a filin ta na Mahaha sports complex dake Kofar Na’isa a jihar Kano.

Wasanni

Rashin kyan fili ne ya janyo Kano Pillars ta yi rashin nasara – Ibrahim

Published

on

Mai horas da kungiyar Kano Pillars, Ibrahim A Musa, ya ce sakamakon ruwan saman da a ka yi ya sanya kungiyar ta Kano Pillars ta yi rashin nasara a hannun Rivers United.

Ibrahim A Musa ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake ganawa da jami’in hulda da jama’a na kungiyar, dris Lirwani Malikawa, bayan kammala wasan da Kano Pillars ta yi rashin nasara da ci 2 da nema a hannun Rivers United a wasan mako na 26 na gasar cin kofin kwararru ta kasa wato (NPFL) wanda wasan ya wakana a Adokiye Amiesimaka dake Fatakwal.

Ga cikakken jawabin mai horas da Kano Pillars, Ibrahim A Musa da ya yi bayan kammala wasan ta.

Continue Reading

Wasanni

Umar Gago Challenge Cup: Kungiyoyi 24 za su fafata a gasar

Published

on

A ranar Juma’a ne za a fara gasar cin kofin kalubale na Umar Gago Challenge Cup wanda kungiyoyi 24 ne za su fafafata a gasar.

Ga jerin rukunin gasar:

Tukunya ta Daya

1- Kwankwasiyya United

2- Jakokore Yamadawa

3- Golden Bullet

4- Hotoro United

5- FC Hart

6- Darma United

Tukunya ta Biyu

1- Highlanders

2- Dorayi warriors

3- Kano Ambassador’s

4- Alfindiki United

5- Ithad Mandawari

6- Gwale United

Tukunya ta Uku

1- Soccer Strikers

2- Ashafa United

3- New Star Rijiyar Zaki

4- Rijiyar Zaki Stars

5- KC Sudawa

6- Top Star Panshekara

Tukunya ta Hudu

1- Dabo Babeis

2- Kano Municipal

3- Dorayi Babba Lions

4- Chiranci United

5- Dorayi Babba Warriors

6- Red Elephant

Za a fara wasan farko tsakanin Kwankwasiyya da Golden Bullet a filin wasa na Dorayi Babba Lions dake makarantar G.G.S.S Dorayi Babba kusa da masallacin Juma’a na Dan Sarari a ranar Juma’a.

Continue Reading

Wasanni

Wasan sada zumunci da a ke fafatawa a Kano

Published

on

A wasan sada zumunci da a ka fafata a jihar Kano, kungiyar kwallon kafa ta FC Rising Stars ta yi rashin nasara a hannun Dorayi Warrios da ci 2 da 1.

Yayin da Dorayi Babba Lions ta yi canjaras da Ungoggo Babies.

Darma United ta samu nasarar doke Brilliant Tukuntawa da ci biyu da nema.

Ita kuwa Abiyati Kurna za ta kece raini da FC Ashafa Makwarari Feeder a filin wasa na Abiyati dake Kurna Babban Layi a yammacin ranar Adabar.

A ranar Lahadi ne K.C United za ta barje gum da Dukawuya United a filn wasa na F.C.E.

Kungiyar kwallon kafa ta Red Elephant za ta kara da Amir Boya Amotsa filin wasa na Ramcy ranar Asabar.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!