Connect with us

Wasanni

Freedom Galaxy ta lashe kofi a hannun Malaga Indabawa

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Freedom Galaxy ta samu nasarar lashe kofi bayan da ta doke kungiyar kwallon kafa ta Malaga Indabawa a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Wasan dai an fafata shi ne a filin wasa na kungiyar kwallon kafa ta Admiral dake Kwalejin Rumfa da yammacin ranar Laraba.

Wasan an tashi Freedom Galaxy na da 1 Malaga Indabawa na da 1 bayan da dan wasan Freedom Galaxy Abubakar Messi ya zura kwallo daya a ragar Malaga Indabawa.

A bugun daga kai sai mai tsaron raga ne kungiyar kwallon kafa ta Freedom Galaxy ta samu nasarar lashe gasar a karo na farko a hannun Malaga Indabawa da ci 5 da 4.

Wasanni

Rashin kyan fili ne ya janyo Kano Pillars ta yi rashin nasara – Ibrahim

Published

on

Mai horas da kungiyar Kano Pillars, Ibrahim A Musa, ya ce sakamakon ruwan saman da a ka yi ya sanya kungiyar ta Kano Pillars ta yi rashin nasara a hannun Rivers United.

Ibrahim A Musa ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake ganawa da jami’in hulda da jama’a na kungiyar, dris Lirwani Malikawa, bayan kammala wasan da Kano Pillars ta yi rashin nasara da ci 2 da nema a hannun Rivers United a wasan mako na 26 na gasar cin kofin kwararru ta kasa wato (NPFL) wanda wasan ya wakana a Adokiye Amiesimaka dake Fatakwal.

Ga cikakken jawabin mai horas da Kano Pillars, Ibrahim A Musa da ya yi bayan kammala wasan ta.

Continue Reading

Wasanni

Umar Gago Challenge Cup: Kungiyoyi 24 za su fafata a gasar

Published

on

A ranar Juma’a ne za a fara gasar cin kofin kalubale na Umar Gago Challenge Cup wanda kungiyoyi 24 ne za su fafafata a gasar.

Ga jerin rukunin gasar:

Tukunya ta Daya

1- Kwankwasiyya United

2- Jakokore Yamadawa

3- Golden Bullet

4- Hotoro United

5- FC Hart

6- Darma United

Tukunya ta Biyu

1- Highlanders

2- Dorayi warriors

3- Kano Ambassador’s

4- Alfindiki United

5- Ithad Mandawari

6- Gwale United

Tukunya ta Uku

1- Soccer Strikers

2- Ashafa United

3- New Star Rijiyar Zaki

4- Rijiyar Zaki Stars

5- KC Sudawa

6- Top Star Panshekara

Tukunya ta Hudu

1- Dabo Babeis

2- Kano Municipal

3- Dorayi Babba Lions

4- Chiranci United

5- Dorayi Babba Warriors

6- Red Elephant

Za a fara wasan farko tsakanin Kwankwasiyya da Golden Bullet a filin wasa na Dorayi Babba Lions dake makarantar G.G.S.S Dorayi Babba kusa da masallacin Juma’a na Dan Sarari a ranar Juma’a.

Continue Reading

Wasanni

Wasan sada zumunci da a ke fafatawa a Kano

Published

on

A wasan sada zumunci da a ka fafata a jihar Kano, kungiyar kwallon kafa ta FC Rising Stars ta yi rashin nasara a hannun Dorayi Warrios da ci 2 da 1.

Yayin da Dorayi Babba Lions ta yi canjaras da Ungoggo Babies.

Darma United ta samu nasarar doke Brilliant Tukuntawa da ci biyu da nema.

Ita kuwa Abiyati Kurna za ta kece raini da FC Ashafa Makwarari Feeder a filin wasa na Abiyati dake Kurna Babban Layi a yammacin ranar Adabar.

A ranar Lahadi ne K.C United za ta barje gum da Dukawuya United a filn wasa na F.C.E.

Kungiyar kwallon kafa ta Red Elephant za ta kara da Amir Boya Amotsa filin wasa na Ramcy ranar Asabar.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!