Connect with us

Labarai

Tsofaffin Alƙalai: Mu na bukatar Ganduje ya waiwaye mu – Kungiyar Alƙalai

Published

on

Kungiyar Alƙalai masu ritaya ta jihar Kano Alƙali ta bukaci gwamnati, da ta wai-wayi tsofaffin Alƙalan jihar wajen basu kuɗaɗen da akan basu bayan da su ka yi ritaya.

Shugaban kungiyar, Alƙali Musa Abdullahi mai ritaya ya bukaci hakan, ta cikin shirin Doka Gatan Al’umma na nan gidan rediyon Dala FM Kano, wanda aka gudanar na musamman a ranar Laraba.

Ya ce, “Izuwa yanzu wasu daga cikin Alƙalan da suka kammala aiki, sun haura shekaru shida ba tare da an basu garatutinsu ba, wanda hakan tasa mu ka faɗa cikin wani hali”. A cewar Alƙali Musa Abdullahi mai ritaya.

Da yake nasa jawabin Sakataren Ƙungiyar, Alƙali Sani Ahmad Chiranci mai ritaya kuma lauya a yanzu cewa ya yi, “Sashi na sha biyu na kundin tsarin doka,ya ce gwamnati ta kula da Alƙalai ta kowanne ɓangare, sai dai a halin yanzu  Al’amarin ya sha banban, saboda haka muke kira ga gwamnati da ta wai-wayi al’amarin”. Inji Alƙali Sani Ahmad Chiranci.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Shima a nasa ɓangaren Tsohon Alƙali Abdullahi Mai Tama ya bayyana cewar, yanzu haka ƙungiyar ta shirya buɗe makaranta da za ta rinƙa bayar da ilmin rabon gado ga ma’aikatan Shari’a, dama sauran al’umma baki daya.

 

 

Labarai

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.

Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.

Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.

Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala

Published

on

Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.

“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.

Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.

Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.

Continue Reading

Labarai

Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge

Published

on

Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.

Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.

Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.

A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.

Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.

Continue Reading

Trending