Connect with us

Labarai

Hisba za ta dauki mataki kan kananan ‘yan mata masu barin gidajen iyayen su – Ibni Sina

Published

on

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta koka mutuka da yawaitan ‘yan mata masu kananan shekaru da kan bar gidajen iyayen su su tare a wurin samarin su tsawo lokaci.

Babban Kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina ne ya koka a kan hakan, ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Lawan Ibrahim Fagge, aka kuma rabawa manema labarai, duba da yadda hukumar ta Hisbah ke ci gaba da da samun yawaitan aikata irin wadannan laifi a tsakanin matasa.

Haka  zalika, Harun Ibn Sina ya  sake koka wa a kan tsohuwar ta’adar tura yara masu karancin shekaru birni da sunan ‘yar aiki ko aikatau.

Ya na mai cewa, “Hukumar Hisbah za ta dauki matakan ba Sani babu sabo, a kan dukkan matashi ko mashiyar da Dakarun hukumar su ka kama ya na aikata irin wadannan laifuka”. Inji Ibni Sina.

Daga bisani, Babban kwamandan ya bukaci ‘ya’ya da su tabbatar da kara yin biyayya ga iyaye da bin umarnin su sau da kafa kamar yadda, Allah ya umarta, domin samun rayuwa mai cike da albarka.

Labarai

Aure: Haramin ne mace ta fita daga gida ba tare da izini ba – Dr Abdallah

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Usman Bin Affan dake unguwar Gadan Ƙaya, Dakta Abdullah Usman Umar ya ce, ba dai-dai ba ne mata su rinƙa fita duk inda su ka so zuwa, ba tare da neman iznin mazajen su ba.

Dakta Abdallah Gadon Ƙaya ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Rayuwa Abar Koyi na nan gidan rediyon Dala FM, wanda ya gudana da safiyar Juma’a.

Ya ce”Fitar da wasu matan ke yi ba tare da neman izinin mazajen su ba yin hakan saɓawa ne, kuma bai kamata mata su rinƙa cin mutuncin mazajen su ba, domin kuwa raina miji raina addini ne”. A cewar Dakta Aballah.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Dakta Abdullah Gadan Ƙaya, ya kuma shawarci magidan ta, da su kaucewa yin azalo ga matan su, domin yin hakan ba dai dai ba ne ba a tsarin addinin Musulunci.

Continue Reading

Labarai

Shan Kwayoyi: Kowa sai ya bayar da gudunmawa a bangaren- Farfesa Hafsat Ganduje

Published

on

Matar gwamnan Kano, Farfesa Hafsat Umar Ganduje, ta ce yaki da shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa ba zai tabbata ba, har sai kowa ya bayar da gudunmawar sa a fannin.

Farfesa Hafsat Ganduje ta bayyana hakan ne, a yayin wani rabon bayar da tallafin kekuna da kayan karatu ga dalibai, wanda ya gudana a  hukumar Shari’a.

Ta ce”Gwamnatin Kano na iya kokarin ta wajen yaki da shan miyagun kwayoyi, amma duk da haka sai kowa ya shigo ya bayar da ta sa gudunmawar, yanzu haka gwamnatin Kano ta kara daura dammara wajen gyara tare da samar da kayayyakin da a ke da bukata a makarantar gyaran hali dake karamar hukumar Kiru”. Inji Farfesa Hafsat Ganduje.

Wakilin mu Ahmad Rabi’u Ja’en ya rawaito cewa, a yayin bayar da tallafin an raba kekunan hawa da jakunkuna na makaranta ga wasu daga cikin daliban Firamare.

Continue Reading

Labarai

Rahoto:  Mu kara godiya ga Allah da mu ka sake ganin watan Mauludi – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Ammar bin Yasir da ke unguwar Gwazaye gangar ruwa a karamar hukumar Gwale, Malam Zubairu Almuhammdi ya ce, musulmi su kara jaddada godiyar su kasancewar su na cikin al’ummar manzon Allah (S.A.W).

Malam Zubairu Almuhammdi, ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yi wa gidan rediyon Dala FM karin bayanin abin da hudubarsa ta kunsa.

Domin jin cikakken bayanin hudubar saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!