Connect with us

Labarai

Budurwa ta kona gidan su cikin dare domin guduwa wajen saurayin ta

Published

on

An yi zargin wata matashiyar budurwa ta bankawa gidan su wuta sannan ta haura katanga cikin dare ta hau mota ta gudu zuwa wajen saurayin ta.

Tunda fari dai saurayin ya hadu da budurwar a garin Wudil, har su ka yi musayar lamba, kuma tun daga lokacin aka yi zargin idon matshiyar ya rufe, ta gudu ta tafi wajen saurayin ta, kamar dai yadda mahaifiyar ta sheda, bayan da hukumar hisba ta tattaro su gaba daya.

Ta na mai cewa, “Ta bankawa gidan wuta ne, kan wai saboda me aka hana ta ta je wajen saurayin ta”.

Ta kuma ce, “Haka aka yi ta fama da ita har cikin azumi, sai ta yi amfani da alfarmar watan cikin dare, ta kama Katanga ta haura ta tafi”. A cewar mahaifiyar matashin.

Sai dai koda aka waiwayi matashiyar ta ce, Kawai tsabar soyayya ce, kuma yanzu ma so take su yi aure, kuma in ba shi din ba sai dai ko rijiya, duk da ta kafa sharadin ba sai an nadi muryarta ba.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Abdullahi Sorondinki, ya je ga saurayin wanda ya bayyana cewar, “Soyayya ce kawai domin ta ce za ta yafe min lefe, saboda haka fata na a yanzu Ubangiji ya yafe mana abunda mu ka yi a baya, ita kuma hisba ta dora mu a tsarin addinin Islama mu yi aure”. Inji saurayin.

Hukumar hisbar ta jihar Kano ta bakin babban Kwamandan ta Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina ta ce, su na kan bincika al’amarin, gabanin su dauki matakin da ya dace.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Labarai

Kungiyoyin tallafawa marayu ku hade kan ku wuri guda – Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil, ya yi kira ga kungiyoyin tallafawa marayu dake jihar Kano da su hade kan su waje guda domin yin magana da murya daya.

Malam Ibrahim Khalil, ya yi kiran ne yayin da gamayyar Kungiyar Tukuntawa Foundation dake tallafawa marayu da marasa karfi a yankin unguwar Tukuntawa dake karamar hukumar birni a jihar Kano ta kai masa ziyara a ranar Talata.

Ya ce, “Hadewar kungiyoyin waje guda ne zai sa a rinka ganin amfanin kungiyoyin ta hanyar yin shugaba guda daya a jihar Kano, sai kuma masu taimaka masa a kananan hukumomi”.

Ya kuma ce, “Naji dadi da ku ka yi tunanin taimakawa al’ummar yankin ku, domin hakan shi ke da wahala a cikin al’umma, da za a ce kowa ya na tunanin al’ummar sa, ba shakka da an zauna lafiya da kuma samun ci gaba a tsakanin al’umma”. Inji Malam Ibrahim Khalil.

Malam Ibrahim Khalil, ya kuma ja hankalin ‘yan kungiyar da su kasance masu biyayya ga shugabanci da kuma girmama manyan unguwa.

 

 

 

 

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Mu na bukatar gwamnatin Kano ta gyara hanyar Doka da Riruwai – Majalisa

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci  gwamnatin jiha da ta karasa aikin titin da ya hade garuruwan Doka da Riruwai dake karamar hukumar Doguwa.

Bukatar ta biyo bayan kudurin da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Doguwa Salisu Ibrahim Muhammad ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar  Zubairu Hamza Massu.

Ya ce, “Idan aka gyara wannan hanya za ta taimaka wajen ci gaban al’ummar yankin”. Inji Salisu Ibrahim.

Wakiliyar mu a majalisar dokokin jihar Kano Khadija Ishaq Muhammad  ta rawaito cewa, kudurin ya sami goyon bayan wakilin mutanen kananan hukumomin Rimin Gado da Tofa, wanda daga bisani zaman majalisar ya bukaci gwamnatin jiha da ta ci gaba da samarwa al’umma ababen more rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Al’umma ku rinka tanadar lambobin mu – Hukumar kashe Gobara

Published

on

Hukumar kashe Gobara da kai agajin gaggawa ta jihar Kano ta danganta asarar rayuka da dukiyoyi a kan rashin tanadar lambobinta na kira domin neman dauki har sai idan iftila’i ya faru.

Babban Daraktan hukumar Alhaji Hassan Ahmad Muhammad ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai a ofishin sa.

Ya ce, “Kame-kamen neman lambar hukumar a lokacin da iftila’i ya faru ya na kawo jinkiri wajen kai dauki, wanda hakan ke haifar da asarar rayuka da dukiya”. A cewar Alhaji Hassan.

Shugaban ya yi kira ga al’umma da su rika ajiye lambobin hukumar kafin bukatar su ta zo domin ceton rayukan al’umma da dukiya akan lokaci.

Lambobin su ne: 080 98 82 26 31 da 070 26 02 64 00 sai kuma 070 51 24 68 33.

Shugaban hukumar kashe gobarar ta jihar Kano, ya kuma bukaci masu ababan hawa a kan titi da su rika baiwa jami’an hukumar hanya a duk lokacin da suka fita kai agajin gaggawa.

Daga bisani ya kuma nuna gamsuwarsa bisa yanda jami’an tsaro da al’ummar jIhar Kano suke ba su hadin kai.

 

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!