Connect with us

Labarai

Ma’aikatan kotu: Maganar yajin aiki babu batun janyewa – JUSUN

Published

on

Kungiyar ma’aikatan Shari’a ta kasa (JUSUN) ta kira taron gaggawa a shelkwatar ta da ke babban birnin tarayyar Abuja.

A daren jiya Talata ne dai wasu kafofin yada labarai na zamani suka fitar da labarin cewa yajin aikin da kungiyar ta ke yi yazo karshe, hakan na nufin za a bude kotuna a fadin Najeriya.

An dai shiga wata na Uku da fara yajin aikin, sakamakon korafin da ma’aikatan Shari’a ke yi na cewar an hana su yancin gashin kai.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya ziyarci shelkwatar kungiyar a Kano, sai dai ya iske shugabannin kungiyar sun yi bulaguro zuwa Abuja.

Wakilin namu ya kirawo sakataren kungiyar na Kano, Kwamared Sule Ali, Wanda ya ce”Mu na hanyar Abuja an kira mu taron gaggawa. Babu wani karin haske da zan yi a kan taron na mu sai dai ina tabbatar mu ku cewar maganar yajin aiki ba batun janyewa har sai an biya mu bukatun mu wanda kundin tsarin mulki ya ba mu”.

Sakataren ya kuma musanta zargin da wasu mutane su ke yi cewar wai kungiyar ta na yajin aikin ne, domin ganin an ragewa gwamnoni karfin iko.

Sai dai kungiyar ta baiwa al’umma hakuri cewa, dazarar an cimma matsaya komai zai zama tarihi.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending