Connect with us

Labarai

Kotu ta hukunta wasu ‘yan kasuwa da suka rushe Kantinan kasuwa

Published

on

Kotun majistret mai lamba 12 karkashin mai Shari’a Muhammad Jibrin ta zartas da hukunci a kan wasu ‘Yan kasuwa wadanda ‘yansanda suka gurfanar da su bisa laifin hada baki da keta doka.

Kunshin zargin da ake yiwa mutanen ya bayyana cewar, mutanen sun hada baki sun rushe wasu Kantina da ake ginawa a kasuwar Kofar Ruwa a shekarar 2016.

A yayin karanta hukuncin kotun ta bayyana cewar,  ta karbi shaidar da magabatar da kara ya kawo yayin da aka yi watsi da shaidun kariya.

Gabannin zartas da hukuncin lauyan da yake kare su Baristar Murtala Alimi ya roki kotun da ta masu damar biyan tara kasancewar su masu iyali.

Mai shari’a Muhammad Jibrin ya daure su shakara daya ko zabin tara na naira dubu 50 kowannen su a laifin keta yayin da za su kwashe watanni shida-shida a gidan gyaran hali ko zabin tarar dubu ashirin ashirin.

Lauyan gwamnati Lamido Soron Dinki ya roki kotun da ta umarce su su biya masu kara ramko na kantinan da suka rusa Naira miliyan 15 saidai barrister Alimi yayi suka.

Kotun ta sanya ranar 14 ga wannan watan nan na Yuli domin sauraron shaidu akan kudin ramko. Shi kuwa lauyan wadanda aka hukunta Barista Murtala Alimi ya bayyana cewar za su daukaka Kara.

Wakilinmu Yusuf Nadabo ya zanta da daya daga cikin masu kara Alhaji kabiru She-she wanda ya bayyana gamsuwa da hukuncin.

 

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending