Connect with us

Labarai

Shekarar 2020: Kano na kan gaba a masu fama da Maleria – Ma’aikatar lafiya

Published

on

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce a  shekarar 2020 data gabata jihar Kano na kan gaba na adadi mafi yawa na masu fama da cutar Maleria, wanda Najeriya keda kaso 27 a cikin kaso 87 a duniya baki daya.

Babbar Sakatariyar a ma’aitakatar lafiyar Hajiya Amina Aliyu Musa ce ta bayyana hakan yayin kaddamar da gangamin yaki da zazzabin cizon sauro a yau

Ta ce, “Za a yi kwanaki hudu ana gudanar da yaki da zazzabin ciron sauron wanda yara ‘yan kasa da shekara biyar za’a  baiwa maganin zazzabin cizon sauron a fadin jihar Kano”.

Ta kuma ce, “Yin hakan ya biyo bayan yadda ma’aikatar ta lura a shekarar da ta gaba kaso 60 na masu zuwa asibiti a jihar kano suna fama da zazzabin cizon sauron ne”.

Ta kara da cewa, “Ta cire wani kaso da take lura da mata masu juna biyu da kananan yara domin illar da zazzabin cizon sauron yake musu, kuma za’a yi gangamin yaki da zazzabin ne sau 4 a shekarar da muke ciki wanda zasuyi da yan jaridu”. A cewar Hajiya Amina Aliyu.

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending