Connect with us

Labarai

Tsaiko: Abduljabbar ya zargi gwamnatin Kano a kan shari’a

Published

on

A yau Laraba 28-07-2021, babbar kotun shari’ar muslinci ta birni a jihar Kano ta ci gaba da sauraron Shari’ar nan wadda gwamnatin Kano ta gurfanar da Malam Abduljabbar Nasiru Kabara.

Gwamnatin ta na zargin malamin da laifin batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W).

A zaman kotun na yau mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, ya tambayi lauyan gwamnati cewar a zaman da kotun ta yi a baya wanda a ke tuhuma ya musanta zargin da ake masa, domin haka ko kun zo da shaidun.

A nan ne lauyar gwamnati ta shaidawa kotun cewar ba su zo da shaidun ba, domin suna bukatar su rubuta tuhuma daga ma’aikatar Shari’a tun da yanzu takarda tuhuma ta ‘yansanda ce kawai a gaban kotun.

A nan ne lauyan da ya ke kare Abduljabbar, Barrister Sale Muhammad Bakoro, ya bayyana wa kotun cewar masu kara suna son kawo tsaiko tunda Wanda ake Kara ya na tsare a gidan gyaran hali yau kwanaki 12 kenan, amma a ce har yanzu ba su shirya takarda tuhuma ba.

Saboda haka barrister Sale Bakoro ya roki kotun a kan cewar in har kotun za ta daga zaman, to kotun ta umarci masu kara su basu duk wasu takardu da su ka shafi Shari’ar da sunan shaidun da kuma duk wani abu wanda zai taimakawa wanda ake tuhuma, domin kare kansa.

A nan ne lauyar gwamnati ta bayyanawa kotun cewar lauyan wanda ake kara ya yi azarbabi dama duk wannan roke-roke da ya yi munsan su kuma da zarar mun gabatar da tuhuma zai ga mun kawo duk abubuwan da ya roka, domin haka ta jaddada rokonta akan a sanya wata rana.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending